An bayyana ainihin albashin Sarki Sanusi II duk wata (Shaida)
- A makon da ya gabata ne dai aka zargi cewa ana biyan Sarkin albashin naira milyan 12.
- Ga 'pay slip' din Mai martaba Sarkin na Kano masu cewa ana biyansa naira milyab 12, ainahin albashinsa milyan daya ne da dubu dari uku bai kai na marigayi Ado Bayero ba.
A makon da ya gabata ne dai aka zargi cewa ana biyan Sarkin albashin naira milyan 12.
Ga 'pay slip' din Mai martaba Sarkin na Kano masu cewa ana biyansa naira milyab 12, ainahin albashinsa milyan daya ne da dubu dari uku bai kai na marigayi Ado Bayero ba.
Legit.ng ta samu labarin cewa a baya bayan nan ne hukumar EFCC ta yi yunkurin binciken masarautar Kano bisa zargin cewa an yi faccaka da kudade har Naira miliyan dubu hudu.
Kanawa da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu, kowana lungu da sako mutane ke taruwa a jihar ta Kano, fadin badakala da ta kunno kai a masarautar Kano suke yi, kamar yadda majiyar mu ta rawaito.
KU KARANTA: Saraki ya ziyarci asibiti
Wani Ibrahim Abdullahi yace tarihi ne ke maimaita kansa saboda sarkin yanzu Muhammad Sanusi ll ba mutum mai tsoro ba ne, ya gaji kakansa sarki Sanusi na daya kuma shi mutum ne mai tsayawa kan gaskiya.
Yayinda Umar Ibrahim Usman ke cewa yana goyon bayan gwamnati ta binciki lamarin saboda faccaka tayi yawa a Najeriya, don haka ya kamata a tabbatar da gaskiyar lamarin.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng