Rikici a Jahar Delta: Daruruwan Hausawa sun nemi dauki ofishin yan sanda
- Rikici ya barke a garin Abraka da ke karamar hukumar Ethiope East a jahar Delta a sakamakon gillewa wani matashi kai da fulani makiyaya suka yi.
- Matashin mai suna Solomon Ejoor dai ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya tafi daji domin ya taho da mahaifiyarsa gida a sakamakon harbe harbe da Fulani ke yi a yankin.
Legit.ng ta samu labarin lamarin ya fusata mutanen garin inda suka fito zanga zanga, suka kwace gawar matashin daga hannun ‘yan sanda suka kai ta fadar sarkin garin da nufin cin zarafinsa, tunda a al’dance, sarkin baya ganin gawa.
Sun yi ta fashe fashen motoci da sauran kayayyakin da ke fadar, kuma saura kiris su cinna mata wuta ba dan sojoji sun kai wa sarkin dauki ba.
Sun zargi sarkin garin da gwamnan jahar da yin shiru yayin da Fulani ke ci gaba da kashe mutanen su.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya yi kamari har sai da Hausawan da ke garin fiye da dari suka buya a ofishinsa ‘yan sanda, gudun kada a far masu.
KU KARANTA: Halima Atete ta illata Nafisa Abdullahi
Kwamishinan yan sandan jahar Zannan Ibrahim ya tabbatar da faruwar wannan lamari.
Ya shaidawa jaridar Vanguard cewa ya bukaci a yi bincike a jejin domin a tabbatar cewa Fulani ne suka aikata laifin, domin a fadar sa, akwai rikici tsakanin ‘yan jahar Edo da Delta akan mallakar wannan sashe na daji.
Haka kuma ya ce zai tura jami’an yan sanda wajen iyalin mamacin domin su yi masu jaje.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng