Kisan Sheikh Ja'afar: Shekarau da Goje sunce babu ruwan su

Kisan Sheikh Ja'afar: Shekarau da Goje sunce babu ruwan su

- Tsohon gwamnan Gombe Sanata Danjuma Goje da tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau sun nisanta kansu da kisan mashahurin malamin addini Islama Sheikh Ja'afar Mahmud Adam da aka kashe yana bada sallah a Kano.

- Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta samu wasu takardu da ke alakanta tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau da kashe Sheikh Malam Ja’afar a dirar mikiyar da jami’anta suka yi wa gidan Sanata Danjuma Goje.

Legit.ng ta samu labarin cewa Sanata Goje ya shaidawa majiyar mu cewa wannan wani yunkuri ne na ba ta masa suna.

“Ni ban san wannan takardar ba, ban ganta ba, ban san da zamanta ba”, a cewar Goje.

Tsohon gwamnan na Gombe ya bukaci ‘Yan sanda su fito su fadawa ‘Yan Najeriya wanda ya kashe Malam Jafar amma ba shafa masa kashin kaji ba.

Shi ma a nasa bangaren, Malam Ibrahim Shekarau ya karyata zargin kisan Malamin a lokacin da yana gwamnan Kano.

Kisan Sheikh Ja'afar: Shekarau da Goje sunce babu ruwan su
Kisan Sheikh Ja'afar: Shekarau da Goje sunce babu ruwan su

KU KARANTA: Majalisar ta bayyana sadda zata gama aikin kasafin kudi

Kakakinsa Ghali Sadik ya ce wannan tsohon zance ne da aka manta a Kano bayan binciken farko da ‘Yan sanda suka gudanar a 2007, lokacin da aka bi masallatai ana raba takardar da ke zargin Shekarau nada hannu a kisan Sheik Ja'afar.

A cewarsa, watakila takardar da aka rarrabawa mutane a Kano ce a 2007 ‘Yan sanda suka samu a gidan Sanata Goje.

A ranar 13 ga Afrilu aka harbe Malam Jafar yana jagorantar Sallar Asuba a Kano, kuma har yanzu ba a gano wadanda suka kashe shi ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng