A garin wasa da zungureriyar wuƙa, ɗan tauri ya hallaka kansa (Hotuna)

A garin wasa da zungureriyar wuƙa, ɗan tauri ya hallaka kansa (Hotuna)

- Dan tauri ya gamu da ajalinsa wajen wasa da wuka

-Shi dai wannan dan tauri ance yayi kaurin suna wajen wasa da wukake

- Yansanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Wani dan tauri a kasar Thailanda da yaci maganin karfe ya mutu har lahira bayan wata wuka daya daba ma kansa a kirji ta ci shi.

Wannan dab tauri mai suna Theprit Palee mai shekaru 25 ya kasance yana wasa da wuka ne a wajen wani taro a ranar Laraba 26 ga watan Afrilu yayin da mummunan lamari ya auku.

KU KARANTA: An gurfanar da mutane 3 akan laifin satan akuyoyi 9 a Osun

Dan tauri Palee ya saba amfani da zungureriyar wuka wanda yake daba ma kansa a kirji, amma maimakon ta yanka shi, sai ta karye, sai dai a wannan karon an samu akasi, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito.

A garin wasa da zungureriyar wuƙa, ɗan tauri ya hallaka kansa (Hotuna)
Palee yayin wasa

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa a ranar Laraban data gabata ana cikin wasa, yan kallo sun taru suna ta tafi, kawai sai Palee ya soka ma kansa wukar nan, kawai sai ta burma shi, nan fa jama’a sukayi ta kokarin farfado da shi, amma ina, rai yayi halinsa.

A garin wasa da zungureriyar wuƙa, ɗan tauri ya hallaka kansa (Hotuna)
Dan tauri

Shugaban yansandan yankin San Kamphaeng, Inspekta Caiwat Phan yace “Mun samu labarin wani mutum daya kashe kansa da wuka, a yanzu mun fara bincike, kuma muna tuntubar asibtin da aka kai shi.”

Ya margaya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ka san mutumin daya fi kowa karfi a Najeriya?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng