Haihuwar gwanne: Mata ta haifi yan 2 sau shidda (Hotuna)

Haihuwar gwanne: Mata ta haifi yan 2 sau shidda (Hotuna)

- Wata mata a kasar Kenya ta haifi yaya 37

- Matar ta fara haihuwa tana shekaru 13

Haihuwa baiwane daga Allah, yayin da wani ke nema ido rufe, wani kuwa ya samu har ma sun mai yawa.

A haka ne wata mata Mariam Nabatanzi mai shekaru 37 yar asalin kauyen Kambiri a yankin Mukono da ke kasar Uganda, ta yi aure ne tun tana da shekaru 12, kuma ta fara haihuwa tana da shekara 13, kuma ta farad a yan biyu, zuwa yanzu ta haifi yaya 38.

KU KARANTA: Kungiyar Izala ta gudanar da wa’azin ƙasa a garin Maiduguri (Hotuna)

Sakamakon baiwar haihuwa da Allah ya baiwa Mariam, yan kauyensu suka sanya mata suna ‘Nalongo Muzaala Bana’ wato uwar yan biyu, mai haihuwar yan hudu.

Haihuwar gwanne: Mata ta haifi yan 2 sau shidda (Hotuna)
Uwargida Mariam tare da wasu cikin yayanta

Mariam ta haifi:ariam ta haifi:

1. 'yan biyu sau 6

2. 'Yan uku sau 4

3. 'Yan hudu sau 3

4. Ta kuma haifi daidai sau 2

Goma daga ciki mata ne 28 kuma maza. Sannan kuma babban cikin su shekararsa 23, na karshe wata 4, kamar yadda Legit.ng ta samu bayanai.

A wani hira da Mariam tayi tace “Banyi mamakin haihuwar yara dayawa ba, babana ma yayansa 45, kuma daga yan uku, ya biyar, yan hudu sai yan biyu.”

Haihuwar gwanne: Mata ta haifi yan 2 sau shidda (Hotuna)
Mariam

Shima wani likitan mata Charles Kiggundu ya tabbatar da cewa Mariam ta gaji mahaifinta ne.

Shima wani likitan mata Charles Kiggundu ya tabbatar da cewa Mariam ta gaji mahaifinta ne.

Sai dai Mariam ta nuna damuwarta da yawan haihuwan, inda tace tana neman hanyar dakatar da haihuwar haka, musamman yadda mijinta baya kulawa da ita da yaran nata, a yanzu haka babban danta shekarunsa 23.

Babban dan nata Charles Musis yace “Kannena basu san babanmu ba, tun ina shekara 13 dana gansa ban sake ganinsa ba.” Da wannan ne Mariam take ba iyaye shawara da kada su dinga aurar da yayansu da wuri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya ya koka saboda yunwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel