Jiragen ruwa 34 dauke da matan fetur da kayan abinci zasu sauka a Legas
-Ana sa ran shigowan kaya ta tashan jirgin ruwa da ke Legas
-Hukumar kula da tashohin jiragen ruwa ne ta bayyana hakan
Ana sa ranan jiragen ruwa 34 dauke da kayayyakin ma fetur, kayan abinci da sauransu zasu sauka Apapa da tashan Tin-Can tsakanin watan Afrilun 27 zuwa 15 ga watan Mayu.
Hukumar tashan ruwan Najeriya NPA ta bayyana wannan a mujallanta wanda News Agency of Nigeria (NAN) ta samu a yau Alhamis a Legas.
NPA tace jiragen ruwan na dauke da alkama, mai, kifi, karafuna, masara da sauran su.
Takardan ta bayyana cewa jirage 11 sun sauka a yanzu kuma ana sa ran daukan taki, ethanol, kwantena, man jirgin sama, da fetur.
KU KARANTA: Saraki ya kai ziyara asibitn majalisa
An bada rahoton cewa sauran 18 din zasu kawo kwantenoni, alkama, kifaye, man gas, masara, waken soya, taki man fetur.
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng