An koro yan Najeriya 253 daga kasar Libya (Dalili)
- Akalla ‘Yan Nijeriya 253 aka fatattako daga kasar libya a jiya talata 25 ga watan Afrilu
- Tarin wadannan ‘yan Nijeriyan na hade da yara 11 da manya 242 wadanda aka sauke su a filin jirgin saman dake jihar Legas daga jirgin kasar Libya
- An sauke su ne da misalin karfe 8:10 na daren jiya Talata
Akalla ‘Yan Nijeriya 253 aka fatattako daga kasar libya a jiya talata 25 ga watan Afrilu.
Tarin wadannan ‘yan Nijeriyan na hade da yara 11 da manya 242 wadanda aka sauke su a filin jirgin saman Murtala Muhammad International Airport dake jihar Legas daga jirgin kasar Libya mai suna ‘Libyan Airline’ a misalin karfe 8:10 na daren jiya talata.
Legit.ng ta samu labarin cewa Darakta Janar na hukumar kula da ayyukan gaggawa NEMA, Injiniya Mustapha Maihaja ya labarta cewa za a baiwa wadannan yan Nijeriyan da aka fatattako guzurin kudin motan komawa zuwa yankunasu da kauyukansu.
KU KARANTA: An kama wani kato yana lalata da yaro dan shekara 12
Kamata ya yi a sanar da wadannan matafiya masu zuwa neman kudi kasasshen wajen Nijeriya da cewa, za su iya samun fiye da abin da suka je nema kasasshen waje a Nijeriya, in har suka yi hakuri da zama a kasarsu, Nijeriyar yanzu ba irin ta da bace, abubuwan suna canjawa kuma za a samu cigaba in aka yi hakuri, inji daraktan
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Yan Najeriya a filin jirgin sama
Asali: Legit.ng