Farfesa Attahiru Jega ya mayar da martani ga Goodluck Jonathan

Farfesa Attahiru Jega ya mayar da martani ga Goodluck Jonathan

-Farfesa Attahiru Jega yayi raddi ga Goodluck Ebele Jonathan

-Yace babu yadda za'ayi ayi magudi muddin ana amfani da na'urar 'Card Reader'

Tsohon shugaba hukumar gudanar da zabe ta kasa zaman kanta wato INEC,Farfesa Attahiru Jega, ya mayar da martani ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, akan maganganun da yayi game da zaben shugaban kasan 2015.

Jonathan a wata littafi mai suna, Against the Run of Play, wanda Olusegun Adeniyi, ya rubuta yace Jonathan yace Jega ya bashi kunya game da yadda ya gudanar da zaben 2015.

Farfesa Attahiru Jega ya mayar da martani ga Goodluck Jonathan
Farfesa Attahiru Jega

Mai taimakon Farfesa Attahiru Jega na musamman, Farfesa Mohammed Kuna, yayi magana da bakin Jega inda ya mayar da martani akan maganar Jonathan cewa bambancin sakamakon zaben shugaban kasa da nay an majalisu yayi yawa a jihar Kano, kuma wannan alama ce ta magudi.

KU KARANTA: Adamu Mu'azu yayi raddi ga Goodluck Jonathan

Farfesa Kuna yayi watsi da wannan magana idan yace abune mai matukar wuya ayi magudi tuna anyi amfani wannan na’ura ta ‘Card Reader’.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel