Jaki ya zama gwal a Jigawa, nemansa ake ruwa a jallo, kasan dalili?
-Sakamakon cin naman jaki, dabbar tayi tsada, tayi wuyar samu
-A kudancin Najeriya ne dai aka fi cin naman jaki
Farashin Jaki yayi tashi sosai inda ya linka ninkin ba ninkin a kauyen Birniwa na jihar Jigawa sakamakon karuwan masu mu’amala da naman sa a kudancin Najeriya, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
An san dai Jaki dabba ne da ake amfani da shi a Arewacin Najeriya musamman ga manoma a kauyuka wajen daukan kayayyaki, amma wani bincike da NAN tayi a kasuwar dabbobi na Kumda ya nuna farashin Jakkai ya tashi da kashi 200 saboda karuwan bukatarsa.
KU KARANTA: Dangote ya ƙaddamar da kamfanin haɗa manyan motocin Tirela
Babban Jaki da ake siya N20, 000 a baya ya koma N60,000, yan kasuwan sun bayyana ma majiyar Legit.ng cewa a yanzu jama’a da dama sun koma cin naman Jaki, musamman a kudancin Najeriya, hakan ya sanya farashin Jakin ya tashi.
“Muna kai Jakkai sama da 500 a duk sati zuwa kudancin Najeriya daga Jigawa,” inji wani dan kasuwa mai suna Jarma.
Shima wani dan kasuwar Yusuf Kyari yace: “Hadi da karuwar bukatar naman jaki, muma bama samun isassun jakunan kamar yadda aka saba a baya sakamakon rikicin ta’addanci a Arewacin Najeriya.”
Amma a dayan hannun kuma, wani manomi, Isa Modu ya bayyana bacin ransa dangane da tsadar Jaki, inda yace yanzu karamin manomi bashi da hanyar samun siyar Jaki don gudanar da aikin gona, hakan ta sa manoma suka koma amfani da amalanke.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Sana'ar mutanen Ogun, kalla
Asali: Legit.ng