Wani shahararren malamin Islama ya bayyana ayyukan dake kara Imani ga zukata
- Wani shahararren malamin Islama wanda ke zaune garin Abuja mai suna Imam Abdulganiy Abdulraheem ya bayyana wasu kyawawan ayyukan da suke kara imani ga zukatan bayi
- Shi dai malamin har ila yau ya shawarci yan uwa musulmai da su lazimci karatun alqur'ani sannan kuma su yawaita tadabburi a kan ayoyi da halittun Allah sannan kuma su kasance masu ambaton sa a ko yaushe
Wani shahararren malamin Islama wanda ke zaune garin Abuja mai suna Imam Abdulganiy Abdulraheem ya bayyana wasu kyawawan ayyukan da suke kara imani ga zukatan bayi.
Shi dai malamin har ila yau ya shawarci yan uwa musulmai da su lazimci karatun alqur'ani sannan kuma su yawaita tadabburi a kan ayoyi da halittun Allah sannan kuma su kasance masu ambaton sa a ko yaushe.
KU KARANTA: Yawan wutar lantarki ya karu a Najeriya
Legit.ng ta samu labarin cewa Malamin har ila yau ya shawarci mutane da su kasance masu yin sallolin nafila sannan kuma su guji zunubai.
Imam Abdulraheem ya bayyana hakan ne a cikin kasidar da ya gabatar mai taken "Abubuwan dake jawo raguwar Imani ga zukatan bayi" a wani taron kwana 4 da wata kungiya mai suna Organization of Tadhamunul Muslimeen (OTM) ta gabatar a Abuja.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Tsohon direban fasto ya musulunta
Asali: Legit.ng