Hukumar EFCC tayi caraf da likitan Goodluck, ta tasa ƙeyarsa zuwa kotu

Hukumar EFCC tayi caraf da likitan Goodluck, ta tasa ƙeyarsa zuwa kotu

-Hukumar EFCC tayi caraf da likitan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

-EFCC na tuhumarsa da wawuran zambar kudi da suka kai Naira miliyan 260

Hukumar yaki da almundahana da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta tasa keyar babban mai duba lafiyar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gaban babban kotun tarayya kan zarginsa da yin sama da fadi da kudaden al’umma.

EFCC na zargin likitan mai suna Fortunate Fiberesima kan zargin aikata laifuka 6 da suka shafi yin sama da fadi da wasu makudan kudade ta hanyar baiwa kamfaninsa kwangilar naira miliyan 260, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Abinda ya biyo baya, bayan Osinbajo ya kammala murzan Babachir da tambayoyi

Tun a ranar 7 ga watan Maris ne hukumar EFCC ta gurfanar da Fortunate Fiberesima gaban babban kotun tarayya, sai dai alkalin kotun ya bayyana ma EFCC cewa dukkanin laifukan da ake tuhumar Fortunate Fiberesima ba hurumin EFCC bane, sai dai ICPC.

Hukumar EFCC tayi caraf da likitan Goodluck, ta tasa ƙeyarsa zuwa kotu
Likitan Goodluck

Don haka sai alkalin ya bada shawarar kodai a janye karar, ko kuma ayi ma laifukan gyaran fuska. Amma da bayan EFCC tayi ma tuhume tuhumen gyaran fuska ne a ranar Talata 25 ga watan Afrilu, sai wanda ake kara bayan ana karanto masa laifukansa ya musanta laifukan da ake tuhumarsa gaba daya.

Daga nan sai lauyan wanda ake kara U.B Eyo ya bukaci kotu data ba da belinsa, sakamakon bai taba aikata mummunan laifi ba. Amma lauyan EFCC Y.Y Tarfa kiri da muzu ya nuna rashin amincewa da bada belin.

Hukumar EFCC tayi caraf da likitan Goodluck, ta tasa ƙeyarsa zuwa kotu
Asibitin fadar shugaban kasa

Bayan sauraron dukkanin bagarorin, majiyar Legit.ng ta shaida cewar alkali mai shari’a Affen ya yanke hukuncin cewar wanda ake kara ya cigaba da amfani da belin da EFCC ta bashi, daga nan sai ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Yunin bana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

EFCC ta maka tshohon shugaban NNPC gaban kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel