Wani Fasto ya gano gaskiya, ya yi umurni a kone litattafan Baibul din cocin sa

Wani Fasto ya gano gaskiya, ya yi umurni a kone litattafan Baibul din cocin sa

- Kimanin mabiya Cocin ‘House of Prayer Ministries’ da ke Makerere a kasar Uganda, kusan 3,000 zuwa 6,000 sun cika da matukar mamaki

- Fastonsu Aloysius Bugingo ranar bikin Ista ya karbi dubunnan litattafan Baibul dinsu kana ya cinna musu wuta.

- Jarida Zambezi Report, ta ruwaito cewa Faston ya kona Baibul din ne saboda suna karkatar da mutane daga tafarkin Gaskiya

Kimanin mabiya Cocin ‘House of Prayer Ministries’ da ke Makerere a kasar Uganda, kusan 3,000 zuwa 6,000 sun cika da matukar mamaki yayin da Fastonsu Aloysius Bugingo ranar bikin Ista ya karbi dubunnan litattafan Baibul dinsu kana ya cinna musu wuta.

Jarida Zambezi Report, ta ruwaito cewa Faston ya kona Baibul din ne saboda suna karkatar da mutane daga tafarkin Gaskiya.

Legit.ng ta samu labarin cewa ya kara da cewa, littattafan Baibul irin su The King Jame’s version, the New Testament, The Good News Bible an gurbata su.

Wani Fasto ya gano gaskiya, ya yi umurni a kone litattafan Baibul din cocin sa
Wani Fasto ya gano gaskiya, ya yi umurni a kone litattafan Baibul din cocin sa

KU KARANTA: Za'a iya bincikar Jonathan idan an same shi da laifi - Minista

A wani labarin kuma, A safiyar yau Talata Musulunci ya karbi bakuncin wani bawan Allah a Jami'ar Bayero da ke Kano karkashin jagorancin shugabancin Kungiyar Dalibai Musulmi ta kasa reshen Jami'ar (MSSN).

Bawan Allah mai suna Jimoh da farko, ya koma Aliyu bayan ya karbi kalmar shahadar shiga Musulunci.

Aliyu wanda dan asalin kasar Togo ne ya nuna sha'awarsa ta shiga Musulunci bayan ya fahimci cewa Musulunci shine Addinin gaskiya. Inji shi

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma wani Bishop ne da ya musulunta

Asali: Legit.ng

Online view pixel