Lafiya uwar jiki: Anfani 6 da ayaba ke yi a jikin dan adam

Lafiya uwar jiki: Anfani 6 da ayaba ke yi a jikin dan adam

- Mutane da yawa na son cin ayaba amma basu san amfaninta ba, haka na sha ganin tambayoyi akan wai ayaba nasa kiba?

- Amma amsar shine ba dan itaciyar dake sa kiba idan ka cishi kamar yarda aka fiddo shi daga lambu balle har ma yasa kiba.

Ayaba na narkewa cikin mintina (45) sauran 'ya'yan itatuwa na narkewa cikin mintina (15) wannan shine yasa kasa zaka ji wasu na cewa cikina ya cika na ci ayaba amma bayan mintina 45 zasu ji kuma duk ya narke.

Idan mutum zai mai da ayaba da sauran'ya'yan itatuwa abin karin kumallon sa cikin sati daya zaiga chanji wajen Lafiyar sa.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattijan Najeriya ka iya mayar da Ndume – Bukola Saraki

Lafiya uwar jiki: Anfani 6 da ayaba ke yi a jikin dan adam
Lafiya uwar jiki: Anfani 6 da ayaba ke yi a jikin dan adam

1. Ayaba na taimakawa Wajen Rage kiba, ayaba na tattare da kayan gina jiki wanda ba sa saka kiba.

2. Cin ayaba yana kariya daga kamuwa da ciwon daji da na koda kamar yadda bincike ya tabbatar.

3. Haka ma binciken ya tabbatar da ayaba tana daya daga cikin abubuwan da suke sa mutum ya zama mai saurin daukar karatu da dabara.

KU KARANTA: Anfani 6 na yayan lemo keyi a jikin dan adam

4. Sannan kuma shafa ayaba a fata na karama fata kyau da zama sumul sumul.

5. Haka ma Ayaba tana karfafa ido kuma tana kare ido daga cututtuka.

6. Haka ma ayaba tana kare mutum daga cutar Ulcer.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma ku kalli anfanin Kwakumba a jikin dan adam

Asali: Legit.ng

Online view pixel