Wannan damuna, hanya 6 da za ka iya samar da kiwon lafiya ga yara ta amfani da sabon 'ya'yan itacen lemu

Wannan damuna, hanya 6 da za ka iya samar da kiwon lafiya ga yara ta amfani da sabon 'ya'yan itacen lemu

- Har ila yau, za ka iya adana sabon lemu a wani tasa na 'ya'yan itace har ga makonni 2

- Kamar yankin lemu guda yayi wa yaro abin da ya fi 90% cin bitamin C da ake bukata kullum

- Ka dai ba wa yaro gilashin sabo ruwan lemu a kai a kai don ya taimake kara masa jinni

- Ka ba yaro ‘salad’ na 'ya'yan itace dauke da yanka na lemu don matsaloli maƙarƙashiya

Eh, yaranku za su iya ci lemu a kai a kai. Cin lemu ga yara ba wai yana bada lafiya kawai ba, amma shi ne ya kasance hanyan samu sinadirai da amfani sosai ga harkokin kiwon lafiya. Idan kana zabar ingancin lemu, ka tabbata ka zabi lemu wadanda suna da ruwa, masu launi daya a ko’ina ma yara. Har ila yau, za ka iya adana sabon lemu a wani tasa na 'ya'yan itace har ga makonni 2. Ka sa lemu a firiji idan kana son ka ajiye su na tsawon lokaci. Legit.ng ya tara muku amfani 6 na lemu ga yara.

1. Karin lafiya:

KU KARANTA: Ka ji yadda aka yi tsakanin wani ‘Dan bautar kasa da Gwamna Fayose

Lemu na dauke da yawan bitamin da kuma ma'adanai da suna da amfani sosai ga girma, da kuma kiwon lafiya na yara. Kamar yankin sabo lemu guda yayi wa yaro abin da ya fi 90% cin bitamin C da ake bukata kullum, yayin da ‘polyphenols’ dake ciki na taimaka wajen bunkasa da kuma hana cututtuka.

2. Karin jini:

Bitamin C dake cikin lemu na taimaka wajen karin jini da kuma hana bayyanar cututtuka na rashin jini, kamar gajiya a yara. Ka dai ba wa yaro gilashin sabo ruwan lemu a kai a kai don ya taimake kara masa jinni.

Bitamin C dake cikin lemu na taimaka wajen karin jini da kuma hana bayyanar cututtuka na rashin jini, kamar gajiya a yara
Bitamin C dake cikin lemu na taimaka wajen karin jini da kuma hana bayyanar cututtuka na rashin jini, kamar gajiya a yara

3. Magani maƙarƙashiya:

Mafi abinci da yara suke ci basu da isheshen faiba. A sakamakon haka, 'ya'yanku na shan matsaloli maƙarƙashiya. Amfanin lemu ne daya daga cikin mafi tasiri da mafita ga hana hadura a maƙarƙashiya kamar yadda ya hada da yawan faiba.. Za ka iya ka ba wa yaro ‘salad’ na 'ya'yan itace dauke da yanka na lemu don kawar da matsaloli maƙarƙashiya.

4. Lemu na rage matsalolin tari da sanyi:

KU KARANTA: Ka da ka bari a ba ka labari: Amfanin dabino 4 a jikin mutum

Yara sau da yawa na shan hangula da rauni saboda sanyi da tari. Idan k aba su lemu, yana matsayin daya daga cikin mafi kyau magunguna domin rage wadannan matsaloli. Har ila yau, magani na lemu na kare yaro daga cutarwa cututtuka dake tare da tari da kuma sanyi.

Abin da kana bukatar ka yi shi ne, ka cika kofin da sabon ruwan 'ya'yan itace na lemu, ka ƙara cokalin shayi daya na zuma da tsunkule na gishiri, sai ka ba yaro lokacin da yana shan wahala daga tari ko mura.

5. Inganta ido:

KU KARANTA: Wannan abin kunya har ina: Budurwa ta maka wani Malamin addini a Kotu

Lemu shi ne cikkeken tushen bitamin A, flavonoids, phytonutrients, kamar alpha da beta carotenes, lutein, beta-cryptoxanthin, da kuma gina jiki da taimakawa wajen kula da lafiya fata da kuma wajen fitowa na majina na yaro da ido. Amfani da lemu na kuma kara habaka yaronka ta wajen hangen nesa da kuma kiwon lafiya, muhimmanci ido.

6. Maganin gudawa:

Zawo mai tsananin zai iya tabbatar hadari ga yaro ta kiwon lafiya, Idan ka ba yara ruwa na sabon 'ya'yan itacen lemu a kai a kai zai taimaka rage bayyanar cututtuka na zawo. Ka tsarma ruwan sabon 'ya'yan itacen lemu da ruwa har zuwa 50% , sai ka ba yaro. Zai taimaka mishi samun sauki daga narkewa cuta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan Legit.ng bidiyo na nuna yadda ake ci da kuma yanka kayan lambu

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng