Kadan daga cikin gudummawar da Ahmadu Chanchangi ya bayar domin cigaban Musulunci da Al'umma

Kadan daga cikin gudummawar da Ahmadu Chanchangi ya bayar domin cigaban Musulunci da Al'umma

- An yi jana'izar shahararren dan kasuwa Alhaji Ahmadu Chanchangi daya rasu a ranar Laraba

- Jama'a da dama na cigaba da fadin alkhairan sa daya aikata a yayin rayuwarsa

A jiya Laraba 19 ga watan Afrilu ne Allah yayi ma Alhaji Ahmadu Chanchangi rasuwa, Chanchangi hamshakin dan kasuwa ne kuma mai kishin addininsa da al’ummarsa, za’a iya gane haka ta irin taimakon dayake yi ma addinin Musulunci da kuma jama’a gama gari.

Har yanzu dai iyalai, yan uwa da abokan arzikin marigayi Chanchangi na cigaba da nuna alhini tare da jimamin rashinsa, inda jama’a na cigaba da yin dafifi zuwa gidansa dake Kaduna don mika ta’aziyyarsu, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Rasuwar Chanchangi: Buhari ya yabe shi, ya miƙa ta’aziyyarsa

Da haka ne wani marubuci kuma ma’abocin jaridar Rariya, Yusuf Usman Argungu (MNIM) ya aiko da wasu muhimman gudumuwar da Ahmadu Chanchangi ya baiwa addinin musulunci da al’umma gaba daya, kamar haka:

1. Daukar nauyin Tafsir da ake yi a masallacin Sultan Bello dake Kaduna sama da shekara 30.

Kadan daga cikin gudummawar da Ahmadu Chanchangi ya bayar domin cigaban Musulunci da Al'umma
Marigayi Ahmadu Chanchangi

2. Daukar nauyin yada karatukan Sheikh Abubakar Gumi a kafafen yada labarai na tsawon sama da shekaru 30.

3. Bayar da zakka ga mutanen da Allah ya ce a baiwa tsawon sama da shekaru 30.

4. Daukar nauyin karatun marayu da sauran bukatunsu na rayuwa sama da mutum dubu ashirin, da dama daga cikinsu a makarantarsa ta Sheikh Gumi College.

5. Mutum na farko da ya kafa makarantar Boko da ilmin musulunci ga 'ya'yan talakawa kyauta, wato Sheikh Gumi College.

Kadan daga cikin gudummawar da Ahmadu Chanchangi ya bayar domin cigaban Musulunci da Al'umma
Marigayi Ahmadu Chanchangi

6. Shine mutumin da yake kashe dukiyarsa ga gajiyu tsofafi, marayu da yara kanana saboda Allah.

7. Shine mutumin da ya mayar da Unguwar Rigasa cikin birnin Kaduna ta hanyar gina musu gada da tituna da fitar da filaye da layuka kuma ya bayar da su kyauta ga talakawa.

8. Shine mutumin da yace ya sadaukar da dukiyarsa ga taimakon musulunci da sauran jama'an duniya.

9. Shine ya nunawa masu kudin Arewa yadda ake kashe dukiya ga talakawa da gajiyayyu domin Allah.

Wannna kadan kenan daga taskar alherin Alhaji Ahmadu Chanchangi wanda ya rasu a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu.

A wani labarin kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, yan’uwa, da abokan arzikin marigayi Chanchangi, tare da gwamnatin jihar Kaduna da al’ummar jihar gaba daya kan wannan babban rashi da suka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda aka kashe wata tsohuwa a bisa kuskure

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng