Ma’aikatan N-Power sun kawo kukan rashin biyan albashi
-Wasu ma’aikata sunce watanni 5 kenan ba’a biyasu albashi ba
-Shugaban shirin yayi bayani akan rashin biyan albashin
Wasu ma’aikatan shirin N-Power a jihar Kwara sunyi zanga-zanga akan rashin biyan albashinsu tun lokacin da aka dauke su aiki watanni 5 da suka gabata.
Ma’aikatan sunce hakan akeyi tun lokacin da aka fara bayan sun sha bakar wahala wajen bayar da lambar asusun bankinsu da suaransu.
Kakakin kungiyar ma’aikatan, Suleiman Olatunji, yace wadanda wannan rashin biya ya shafa sun je sunyi gyara amma babu abinda akayi musu.
KU KARANTA: Cutar sankarau ta dan lafa a arewacin Najeriya
“Wasu daga cikinmu sunyi gyara a ofishin gwamna da hukumar NOA. Ko yaushe zasuce akwai kuskure daya ko biyu kuma sau 4 muna zuwa gyara.
N-Power ta neme mu da mu aika lambar wayoyinmu kuma duk da hakan basuyi ba,”.
Shugaban shirin na jihar Kwara, Elder Ayobolu Samuel, yace “Lokacin da muka fara shirin a wata Diamba, mutane 5539 ne aka kawo jihar Kwara amma 5021 ne muka tantance. Mun aika sunayensu Abuja amma lokacin da za’a biya kudin wata Junairu, sama da sunaye 2000 sun bace.
Sai muka koma muka duba takardarmu , da aka biya na watan Fabrairu, sunayen sun ragu zuwa 1,508, a watan Maris, sun ragu zuwa 748.
“Saboda haka yayinda wadannan suka zo jiya, mun fada musu su je su duba takardan da muka manna akan dalilin da yasa ba’a biyasu ba.”
https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng