Rasuwar Chanchangi: Buhari ya yabe shi, ya miƙa ta’aziyyarsa

Rasuwar Chanchangi: Buhari ya yabe shi, ya miƙa ta’aziyyarsa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma marigayi Chanchangi

- An yi jana'izar Ahmadu Chanchangi a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’azziyarsa ga iyalan hamshakin dan kasuwa kuma sanannen mai taimakon al’umma Alhaji Ahmadu Chanchangi.

Haka zalika shugaban kasar na yi ma gwamnatin jihar Kaduna tare da al’ummar jihar gaisuwar mutuwar dan tahalikin nan, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kyautata ma talakawa.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

Buhari ya aika da ta’aziyyar ne a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu ta bakin babban mashawarcinsa ta fannin watsa labaru, Garba Shehu, kamar yadda Legit.ng ta samo rahoto.

Rasuwar Chanchangi: Buhari ya yabe shi, ya miƙa ta’aziyyarsa
Alhaji Ahmadu Chanchangi

Shugaba Buhari yana taya abokanansa, iyalai, yan uwa das aura jama’a jimamin mutuwar bawan Allah Ahmadu Chanchangi, tare da fadin zai yi kewar karatuttukan dayake daukan nauyi a gidajen rediyo daban daban.

Buhari yace ba za’a taba mantawa da halin dattakun Ahmadu Chanchangi ba da kuma jajircewarsa wajen neman na kansa ba, daga karshe yayi addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa kuma sada shi da ayyukan alherinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda tsautsayi ya fada kan wata mata

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng