An bayyana dalilin da ya sa farashin Dala ke yin tashin gwaron zabo (Karanta)
- Sakamakon matakan da babban Bankin Najeriya CBN ke dauka na ‘kara sayar da takardar kudin Dalar Amurka ga bankuna da ‘yan canji, yanzu haka darajar Naira na sama na ‘kasa.
- Duk da Miliyoyin Dalar Amurka da Babban Bankin Najeriya ke fitarwa ga bankunan ‘yan kasuwa da kuma masu hada-hadar kudaden kasashen ketare duk mako
Har yanzu farashin Dalar Amurka na ci gaba da hawa kan kudin Naira, ko da yake a baya an samu karyewar kudin na Dala.
Alhaji Bello Datti, masanin tattalin arziki da hada-hadar kudaden ketare da ke Legas, ya ce dalilin da yasa farashin Dala yake sama yana ‘kasa shine saboda yanayin masu karbar kaya, kasancewar rana ‘daya kamfanoni da mutane zasu zo neman sayar kudin Dala wanda idan masu nemanta suka yi yawa, farashinta kan yi sama.
Wasu lokuta kuma idan babu masu neman sayan Dala farashinta kan yi ‘kasa ne.
Legit.ng ta tattaro cewa a cewar babban bankin Najeriya, ya dauki matakin ‘kara yawan Dalolin da ya ke bayarwa musamman ga masu fita kasashen ketare da rijistar makarantu da masu zuwa a duba lafiyarsu da kuma wasu kayayyakin kasuwanci da ba a haramta shigowa da su ba.
KU KARANTA: Ya kamata EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi
Duk da wannan mataki da babban bankin yake ‘dauka masu masana’antu a Najeriya na ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Yayin da masana tattalin arziki da sauran ‘yan Najeriya ke ci gaba da yin nazari game da matakin na CBN, na ‘kara adadin yawan kudaden Dalar Amurka a cikin gida. A waje ‘daya kuma fatan gwamnati shine na ‘kara yawan kudaden da ta ke samu daga cinikin Man Fetur wanda ya karye a kasuwannin duniya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Nan ma dai ana jin ra'ayoyin yan Najeriya ne game da yadda farashin Dala ke shafar su
Asali: Legit.ng