Sabbin hotunan filin sauka da tashin jirage na babban birnin tarayya
- A ranar Talata ne aka bude filin jiragen sama na Abuja bayan an karkare gyare gyarensa
- Kimanin sati 6 kenan tun bayan da aka karkatar da sauka da tashin jirage zuwa jihar Kaduna
A ranar Talata 18 ga watan AFrilu ne aka kammala aikin gyaran filin sauka da tashin jirage na tunawa da Nnamdi Azikwe dake babban birnin tarayya Abuja.
Idan ba’a manta ba dai an rufe filin jirgin ne na tsawon sati 6 don samu daman gudanar da aikin gyare gyare a cikinsa, wanda hakan ya sa aka karkatar da sauka da tashin jiragen zuwa Kaduna.
KU KARANTA: Muddin aka cigaba da tafiya yadda ake yi a Kaduna, APC ba zata lashe jihar ba” – Shehu Sani
Amma kamar yadda hausawa ke cewa, kyawun alkawari cikawa, sai gashi an kammala aikin kwana 1 kafin lokacin da aka sanya za’a kammala shi. Wanda hakan yayi matukar baiwa yan Najeriya mamaki, inda wasu ke ganin wannan basa bambam ne.
Legit.ng ta kawo muku hotunan filin jirgin saman bayan an karkare gyaran.
Ga bidiyon filin jirgin
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ka taba shiga jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja?
Asali: Legit.ng