Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)
-Allah yayi wa matar Sheikh Ibrahim Nyass dake karin Okene rasuwa
- Wasu rahotanni sun yi nuni da cewar Sayyada Bilkisu ta dade da rabuwa da Shehin malamin
Tsohuwar matar fitaccen malamin darikar Tijjaniyya, wato Sheikh Ibrahim Nyass, Bilkisu Okene ta rasu a ranar Lahadi 16 ga watan Afrilu a garin Okene.
KU KARANTA: Karshen duniya! Wata yarinya ta kashe kanta saboda son da take yiwa malamin ta
A ranar Litinin 17 ga watan Afrilu ne aka yi mata jana’iza inda aka binneta a garin na Kogi, sai dai da fari anyi cece kuce tsakanin yan uwanta aka kodai a kai ta can kasar Sanigal ne?
Don a binne ta a daidai inda aka binne tsohon mijinta, shehin malami Nyass.
Legit.ng ta kawo muku wasu daga cikin hotunan jana’izar Sayyada Bilkisu.
Allah ya jikanta, Amin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda direban wani babban faston Najeriya ya musulunta
Asali: Legit.ng