Wani babban jigo a gwamnatin Obasanjo ya rasu

Wani babban jigo a gwamnatin Obasanjo ya rasu

- A labarin da muke samu yanzun daga sassa da dama na nuni da cewa Allah ya yi wa tsohon jakadan Najeriya Ambassador Magaji Muhammad rasuwa a iya

- Ambassador dan asalin garin Dutsinma ne

Ya kuma taba fitowa takarar gwamnan jihar Katsina, sannan kuma dan uwa ne ga Alh Umar Tata tsohon dan takarar gwamnan jihar Katsina da kuma tsohon Gwamnan jihar Ibrahim Shema.

Legit.ng ta tattaro cewa Shi dai Ambasada Magaji Muhammed yayi minista har sau biyu a lokacin mulkin shugaba Obasanjo sannan kuma yayi Ambasada na kasar Najeriya a can kasar Saudiyya duk dai a lokacin mulkin na Obasanjo.

Muna rokon Allah Ya gafarta masa Ya kuma sa ya huta Ameen.

Wani babban jigo a Gwamnatin Obasanjo ya rasu
Wani babban jigo a Gwamnatin Obasanjo ya rasu

A wani labarin kuma, Wata bbabar kotun tarayya da ke jihar Legas ta Najeriya, ta bai wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar wato EFCC izinin adana makuden kudaden da ta gano a unguwar Ikoyi da ke Legas.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da cecekuce dangane da ainihin mamallakin kudaden da yawansu ya zarce Naira Biliyan 10.

KU KARANTA: Sojoji sun damke wani babban Kwamandan Boko Haram

Ana rade-radin cewa, hukumar leken asirin kasar da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike kowanne daga cikinsu na ikirarin cewa, mallakashinshi ne.

An gano kudadden ne a yayin da hukumar ta kai samame a wani gida da aka ce na tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne Ahmad Mu'azu a ranar Laraba, amma daga bisa ya shaida wa manema labarai cewa, tuni ya siyar da gidan na Ikoyi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma iyalan wani mamacin ne ke jimamin mutuwar dan uwan su

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng