Su waye ne ke jagorancin kungiyar Ansaru a Najeriya – Inji ‘yan Najeriya

Su waye ne ke jagorancin kungiyar Ansaru a Najeriya – Inji ‘yan Najeriya

- Kungiyar Ansaru ta zama abin barazana a Najeriya bayan wata 6 da kafa ta

- Kungiyar ta shahara wajen sace-sacen ‘yan kasashen waje a yankin arewacin Najeriya

Kungiyar Ansaru ta zama abin barazana a kasar cikin dan kankanin lokacin da ta shafe tana ayyukanta.

A watan Janairun 2012 ne aka kirkiro kungiyar Ansaru, duk da cewa ba a san ta ba sai bayan wata 6 da kafuwarta, sakamakon sakin wani bidiyo da ta yi da ya nuna yadda 'yan kungiyar suka sha alwashin kai wa Turawa 'yan kasashen yamma hari, domin kare Musulmai a duniya.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a watan Janairun 2012.

"A karon farko muna farin cikin sanar da al'umma kafuwar wannan kungiya wacce aka kafa ta kan hujjoji na kwarai." Inji Legit.ng

KU KARANTA KUMA: Zambia ta turo keyar wani babbar fasto zuwa gida

Sanarwar ta kara da cewa: "Za mu yi aiki ba sani ba sabo a kan komai, domin mu goyi bayan da abin da ayke da kyau mu kuma yada shi, sannan kuma mu kyamaci abin da ba shi da kyau, mu kuma kawar da shi."

Cikakken sunan kungiyar shi ne, Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan, wato: "Kungiyar Kare Musulmai bakake a nahiyar Afirka."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon kashe-kashen rikicin kudancin Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng