Ahmed Musa ya saki matarsa, Jamila
- Dan kwallo Ahmed Musa ya saki uwargidansa saki 3
Shararren dan kwallon Najeriya da kungiyar kwallon kafan Leicester City ya saki matarsa, Jamila, game da cewar SCORENigeria.
Wannan abu na faruwa ne bayan an samu wani sabani tsakaninsa da matarshi a gidansu da ke Ingila a watan nan. Wani majiya ta fadaw SCORENigeria cewa Ahmed Musa ya saki matarsa.
“Ya saketa saki uku, tuni ta koma gida Kano.”
Kamar yadda aka bada rahoto, Ahmed Musa ya rigaya da kai gaisuwa wajen iyalan wata yarinya da ke so.
KU KARANTA: Gwamna El Rufai ya caccaki majalisa kuma
A watan jiya, ya bar filin horon Super Eagles da ke Landan domin zuwa kai gaisuwa wajen iyalan amaryan da yakeso.
Wata majiya mai karfi ya bayyanawa SCORENigeria cewa amaryan yan asalin garin Kalaba ce na jihar Kross RIba. Sunan yarinyan Juliet wacce mazuniyar jihar Legas ce.
Rahotanni ya nuna cewa Ahmed Musa ya bada kyautan gida kuma ya saya mata mota kirar Honda.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng