Gwamnati za ta fara gina wata babbar hanyar jirgin kasa a Najeriya
- Gwamnatin tarayya za ta fara gina wata babbar hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan a ranar juma’a
- Hukumar kula da harkokin jiragin kasa ta kasa (NRC), ta shawarci mutane masu dukiyoyi a filin gina wannan hanyar da suyi hanzari cire dukiyoyin kafin ranar juma’a
Hukumar kula da harkokin jiragin kasa ta kasa (NRC), ta ce an kammala shirin gina hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan wanda zai a fara ranar 14 ga Afrilu.
Legit.ng ta ruwaito cewa babban daraktan hukumar ta NRC, Mr Fidet Okhiria, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu a Legas. Okhiria ya shawarci wadanda suke amfani da filin hukumar su fara cire dukiyoyinsu, don kauce wa halaka su da injin buldoza.
Daraktan ya ce: "Hukumar za ta biya diyya ga wadanda ta shiga yarjejeniya da su. Amma wadanda suka shiga filin ba tare da izinin hukumar ba su tantara nasu da nasu su bar filin kafin ranar juma’a da za a fara aikin ko kuma injin buldoza ta rushe dukiyoyin da ke zaman filin”
KU KARANTA KUMA: Kungiyar matasa masoya Buhari tayi wa yan majalisar dattijai kashedi
Daraktan ya kara da cewa, hukumar ta riga ta fitar da wuraren da a ke bukata kuma mutanen na sane da haka. “Mun gaya musu su cire dukiyoyinsu daga filin kafin buldoza ta fara aiki”.
Hanyar jirgin kasa zai kasance da tashoshin 2 tsakani Legas da Ibadan . Tashoshin za su kasance a Omin Adio da kuma Moniya a garin Ibadan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kali yadda tafiya a jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ya kasance
Asali: Legit.ng