Jihar Kano ta shirya domin kawo zuwa karshe bara a kan titi amma akwai wani kalubale

Jihar Kano ta shirya domin kawo zuwa karshe bara a kan titi amma akwai wani kalubale

- Wasu jihohin ƙasar musamman Kano sun yi dokokin hana bara

- A Najeriya dai, an fi samun gararambar yara a tituna da sigar bara, inda dubban ɗaruruwan

- Sau da dama almajiran na faɗa wa haɗurran rayuwa iri daban-daban

- Yaron wanda aka kai shi Kano almajiranci ya ce sunan ƙauyensu Daburam

- Irin wadannan matsaloli ne dai suka sa gwamnatin jihar Kano ta haramta barace-barace

Yawon bara a tsakanin ƙananan yara na daga cikin manyan ƙalubale da ke addabar arewacin Najeriya, kuma lamarin ya ƙi jin magani duk da illar hakan a tsakanin al'umma.

Wasu jihohin ƙasar musamman Kano sun yi dokokin hana bara da suka tanadi kama almajiri da malaminsa, amma har yanzu matsalar ba ta ragu ba maimakon haka ma ƙara gaba-gaba take yi.

An ware yau Laraba 14 ga watan Afrilu a matsayin ranar tunawa da yaran da ke gararamba a kan tituna a sassan duniya.

KU KARANTA: Rundunar yan sandan Najeriya ta tarwatsa yan shi'a masu zanga-zanga

A Najeriya dai, an fi samun gararambar yara a tituna da sigar bara, inda dubban ɗaruruwan yara ke shafe tsawon wuni suna yawo don neman abinci.

Yaran dai ba sa zuwa makarantun boko don haka babu abin da suka iya a rayuwa sai bara, kuma kalmar da suka fi riƙe wa a baki ita ce "a taimaka mana da abinci."

A Nijeriya dai, an fi samun gararambar yara a tituna da sigar bara, inda dubban ɗaruruwan yara ke shafe tsawon wuni suna yawo don neman abinci
A Nijeriya dai, an fi samun gararambar yara a tituna da sigar bara, inda dubban ɗaruruwan yara ke shafe tsawon wuni suna yawo don neman abinci

Sau da dama almajiran na faɗa wa haɗurran rayuwa iri daban-daban, kamar yadda wani ƙanƙanin yaro ɗan kimanin shekara takwas da ya ɓata a wajen yawon bara a Kano.

Yaron wanda aka kai shi Kano almajiranci ya ce sunan ƙauyensu Daburam amma bai san a cikin jihar da yake ba, ya shafe sama da mako ɗaya yana kwana a titi.

Ya ce ''Makaranta aka kawo ni, ina zuwa yawon bara, lokacin da na ɓata bana kwana a makaranta, a wani budadden wuri nake kwana, ina shimfida leda sai in kwanta.''

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai siyo Jiragen yaki 12 don yakar ta'addanci

Irin wadannan matsaloli ne dai suka sa gwamnatin jihar Kano ta haramta barace-barace, kuma tun bayan fara aikin wannan doka, an kama dubban almajirai da suke kunnen kashi.

Yadda Legit.ng ya samu labari, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ne kwamandan Hizba da ke kamen masu barar ya ce "Kananan yaran (da suka kama ya zuwa yanzu) sun kai dubu biyar da talatin da biyar da dari shida.

"Galibi sun kwararo ne daga jihohi Najeriyar kusan 16, jihar Katsina (daga) nan muka fi samun yara almajirai da yawa''

A cewar darakta Janar na hukumar ta Hizbah Malam Abba Sa'id Sufi suna bin matakai daban-daban idan sun kama masu barar.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ba ta amince a rufe ‘Yan Boko Haram a gidan yari ba

An dai sha gudanar da bincike da nazarce-nazarce da dama gami da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar bara, musamman a arewa.

Cikin aikace-aikacen har da na wani kwamitin wasu fitattun mutane da suka shafe wata takwas suna yi wa gwamnonin arewa nazari kan wasu matsaloli musamman na bara, sannan suka gabatar da rahoto yadda za a magance su.

Sai dai sama da shekara uku da mika wa gwamnonin wannan rahoto har yau babu ko shawara ɗaya da suka fara aiwatarwa.

Ku biyo mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da kuma twitter a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan Legit.ng bidiyo na nuna mata suna zanga zanga a dawo musu da 'yan matan Chibok

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel