Badaƙalar ɗaukan ma’aikata ta dabaibaye hukumar EFCC

Badaƙalar ɗaukan ma’aikata ta dabaibaye hukumar EFCC

- An sauya halastattun jami’an da aka dauka da wasu shafaffu da mai

- Wani lauya yam aka Bukola Saraki da Ibrahim Magu kotu, ya bukace ayi adalci

Hukumar yaki da almundahana da cin hanci da rashawa wato EFCC na fuskantar wata babbar kalubale data danganci daukan sabbin jami’an hukumar da tayi.

Badaƙalar ɗaukan ma’aikata ta dabaibaye hukumar EFCC
Jami'an hukumar EFCC

Majiyar Legit.ng ta shaida mana cewar an sauya sunayen wasu sabbin jami’an da aka dauka su 24 wadanda a yanzu haka suke samun horo a kwalejin horar da hafsan soji na kasa dake Kaduna da wasu shafaffu da mai, masu uwa a gindin murhu.

Lauyan sabbin jami’an da aka cire Olusoji Toki ya aika ma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wasikar koke, inda yaca an sallami wadanda yake wakilta ne bayan sun cika dukkanin wasu sharudda da ake bukatar su samu.

KU KARANTA: Farfesa Ango Abdullahi ya mayar da martani ga Sarkin Kano

Jaridar News Telegraph ta samu kwafin wasikar da lauyan ya aika ma shugaban hukumar EFCC Magu. Wasikar tace: “Sakamakon wadanda nake wakilta sun samu nasara, sai hukumar EFCC ta gayyace su da su halarci jarabawa a ranar 25 ga watan Yuni na 2016, kuma sun je sun yi, daga nan sai EFCC ta gayyace su zuwa inda za’a binciki lafiyarsu a barikin sojojin sama a jihar Kaduna ranar Alhamis 22 ga watan Nuwambar 2016.

“Bayan haka, sai EFCC ta aiko musu da wasikar kota kwana a wayar hannu tana taya su murna, daga nan sai aka gayyace su hirar baka-da-baka a ofishin EFCC dake gida mai lamba 4, layin Wurno Badarawa, Kaduna a ranar 27 ga watan Okotoba 2016., kuma sun halarci zaman. Daga bisani sai EFCC ta sake aike musu da sako ta waya cewa sun samu nasara a daukan ma’aikata masu kwalin difloma, don haka su garzaya NDA don samun horo”.

Badaƙalar ɗaukan ma’aikata ta dabaibaye hukumar EFCC
Shugaban hukumar EFCC tare da Buhari

Sai dai sabbin korarrun jami’an sun bayyana cewar bayan sun kwashe sati uku suna samun horo ne sai EFCC ta kira su su 24m ta bayyana musu wai suna dauke da ciwon koda, da wasu cututtuka dasu basu san dasu a jikinsu ba, don haka sun sallame su.

Ganin haka ya sanya jami’an suka ce basu yarda ba, inda aka basu daman sake yin sabon gwaje gwaje a wani asibiti na daban, amma duk da cewa sakamakon gwaje gwajen bai nuna cewa suna dauke da wadannan cututtukan da EFCC tayi ikirari ba, duk da haka EFCC taki mayar dasu bakin aiki.

duk da kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin Kaakakin EFCC, Mista Wilsom Uwujaren yaci tura, sakamakon baya daukan wayarsa, kuma bai amsa sakon kota kwana da muka ta aika masa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda EFCC ta gurfanar da jami'an INEC kan zargin cin hanci

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng