An kara kudin kujerar Hajji a Kamaru

An kara kudin kujerar Hajji a Kamaru

- Ma'aikatar harkokin cikin gida a Kamaru mai kula da tsara safarar maniyyata zuwa aikin hajji ta sanarwa wa maniyyatan hajjin bana cewa kudin kujerar Makkah ta karu da 282.000 FCFA

- Ana sa ran maniyyata 3,500 daga kasar Kamaru ne bana za su je sauke faralli a Mecca

An kara kudin kujerar Hajji a Kamaru
An kara kudin kujerar Hajji a Kamaru

Ma'aikatar harkokin cikin gida a Kamaru mai kula da tsara safarar maniyyata zuwa aikin hajji, ta fitar da sanarwa in da ta ke shaida wa maniyyatan bana cewa kudin kujerar Makkah ya karu da 282.000 FCFA.

Wannan karin ya biyo bayan faduwar da dala ta ke yi, da bullo da wani sabon tsarin da aka yi a Arafat, da kuma karin kudin gidace.

Tuni dai ma'aikatar ta bayar da umarnin fara yiwa maniyyatan bana rijista.

A bana ma dai kamfanin jirgin saman kasar ta Kamaru wato Camair-Co da hadin gwiwar na kasar Saudiyya Flynas ne za suyi jigilar alhazan zuwa kasa mai tsarki.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya nada sababbin shugabannin hukumomi da ma’aikatun ma’aikatar Ilimi

Ana dai bukatar adadin alhazan bana daga Kamaru 3,500, dan haka hukumar kula da alhazan kasar ta bukaci duk wani maniyyaci da ya yi kokarin kammala biyan kudin kujerarsa kafin ranar 15 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki.

Hukumar ta ce idan har aka samu adadin da ake bukata na alhazan , to za a rufe biyan kudin kujera a kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa

Asali: Legit.ng

Online view pixel