An bani yan matan Chibok 2- Dan Boko Haram kirista

An bani yan matan Chibok 2- Dan Boko Haram kirista

- Yan Boko Haram sun damke Joseph David a garin Mubi tun yana dan shekara 22

-Ya zama Kwamandan Boko Haram kuma yana amsan albashi N500,000 a wata

- Kuma an bashi kyautan yan matan Chibok biyu

An bani yan matan Chibok 2 a matsayin kuyangu - Kwamandan Boko Haram kuma Kirista
An bani yan matan Chibok 2 a matsayin kuyangu - Kwamandan Boko Haram kuma Kirista

Yayinda yan Najeriya ke sauraron dawowan yan matan Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014 , wani Kwamandan Boko Haram yace an bashi kyautan biyu a matsayin kuyangu.

Jaridar The Nation ta samu rahoton cewa Joseph David, Kirista kuma dan Boko Haram yace an bashi kyautan yan matan Chibok din ne a matsayin sa na Kwamandan Boko Haram bayan ya auri wata Faridah.

KU KARANTA: Akwai almajirai milyan3 a Kano

David wanda yayi ikirarin cewa shi dalibin kwalegin fasahan jihar Adamawa ne, yana hannun hukumar Sojin Najeriya.

Yace yana karban albashi N500,000 a wata kuma wani zubin ma da kudaden kasan waje ake biyanshi.

Joseph David yace sun samu sabani da Shugaban su Abubakar Shekau ne saboda yadda yake kula da matansa. Sai ya kwace dukkansu guda 3.

Yace : "Shekau bai yarda da ni ba. Wata rana yace ya san zan gudu in koma Najeriya. "

“Ina neman gafara akan abubuwan da nayi, innama nayi su ne saboda kare rayuwata."

Yan matan har yanzu suna dajin Sambisa.

A bangare guda, jaridar Legit.ng ta tattaro muku cewa yan matan Chibok din da aka ceto guda 21 a watan oktoban 2016, an sanya su a makaranta domin karashe karatunsu.

Tun lokacin da aka sake su, har yanzu gwamatin tarayya tayi shiru akan al'amarin.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng