Saura kiris in gaji marigayi Janar Abacha - Janar Bamaiyi
- Tsohon hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya, Janar Ishaya Bamaiyi, ya bayar da labari tiryan-tiryan na yadda manyan hafsoshin kasar nan suka rika tafka rikici
- Tuggu da tirka-tirkar wanda zai zama shugaban kasa bayan mutuwar tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, wanda ya mutu ranar 8 ga Yuni, 1988
Legit.ng ta samu labarin Bamaiyi, wanda tsohon Laftanar Janar ne, ya bayyana wannan kwamacala ce a cikin wani littafi da ya rubuta da Turanci, mai suna “Vindication of a General” wanda aka kaddamar a ranar Alhamis da ta gabata, a Abuja.
Ya yi bayanin cewa, bayan rufe gawar Abacha a Kano, a wannan ranar sai manyan hafsoshin sojojin kasar nan suka koma Majalisar Koli a fadar Shugaban Kasa, inda suka yi taro domin a fito da wanda zai zama shugaba.
KU KARANTA: Jami'an tsaro ke kara rura wutar rikicin Kaduna
Ya ce duk da cewa shi ba shi da muradin son zama shugaban kasa, sai aka fi maida karfi wajen zaben Babban Hafsan Tsaron Kasa na lokacin, Abdulsalami Abubakar, Ministan Abuja a lokacin, Jeremiah Useni da kuma shi Bamaiyi din. Haka Bamaiyi ya bayyana a cikin shafi na 252.
Ya kara da cewa duk da rashin sha’awar shugabanci da ya yi, matsalar da ya ke da ita dangane da Abdulsalami, ita ce an taba kama shi dumu-dumu da laifi bayan wata kotun soja da aka kafa ta binciki yadda ya yi harkallar kudaden albashin sojoji tsakanin 1970 zuwa 1972. Wannan dalilin ne ya ce ya yi tunanin da wuya idan ma ya ce a zabi Abdulsalami, wasu ba za su amince ba.
Sai da aka yi ta faman shawo kan manyan hafsoshin nan domin su amince da Abdulsalami ya zama shugaban kasa,. Dalili kenan aka je da Bebul da Alkur’ani a wurin rantsuwar.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Ga wani dan Najeriya nan kuma da yace idan zai y sata to fa ba wanda zai hana shi
Asali: Legit.ng