Hah ha! Abinci Najeriya 4 da bai kamata ka ci ba a ranar bikin auren ka

Hah ha! Abinci Najeriya 4 da bai kamata ka ci ba a ranar bikin auren ka

- Idan kana da kyau, za ka ji da kyau', jin kyau yana da mafi yi tare da jikinka fiye da kamannuna

- Suna da dadi amma daga baya, zaka fara neman bayan gida domin ciki ya murdaka

- Barkono ya iya damun ciki, kuma ba abin da kana so a ranar kenan ba

Kar ka taba wayannan abinci a ranar babban bikin ka
Kar ka taba wayannan abinci a ranar babban bikin ka

Bikin aure ne babban biki ne kowa ya san muhimmanci shi hada amarya da ango. Ya kamata muatnen 2 nan su kula da irin abinci da za su ci a ranar.

Sabanin da abin da mutane suka sani, 'idan kana da kyau, za ka ji da kyau', jin kyau yana da mafi yi tare da jikinka fiye da kamannuna.

KU KARANTA: Yaro dan shekara 13 ya rataye kansa a jihar Sokoto

Idan ka ci wani abu da ya bata maka ciki, babu shakka ba zaka ji kyau ba kuma zai kawo karshen dãɗi na lokacin.

Legit.ng yana da wani jerin 4 irin abinci da ya kamata ka kauce wa domin gudu wa ciwon ciki:

1. Wake/Moin-moin: Kamar yadda gwaten wake da moin moin na da dadi, ya kamata ka kauce wa abinci 2 nan kamar kana gudun maita ne a babban ranar ka. Suna da dadi amma daga baya, zaka fara neman bayan gida domin ciki ya murdaka.

KU KARANTA: Abin al-ajabi: Wani yaro mai shekara 20 ya yanka Mahaifiyar sa

2. Miyan kayan lambu: Ana amfani da miyan ne domin wanke ciki da kuma rãyar da tafiya na hanji. Don haka yana da shakka wajen sa a baki a ranar bikin ka. Idan ka ci shi da safe da kuma bai dameka a lokacin ba, zai dameka a daren biki, kuma ba shi da kyau hakanan.

3. Musamman abinci mai kayan yaji da dai sauransu miyan barkono: Ko da kana son abinci mai barkono, kuma kana da cikin karfe, kar ka yi kusa da shi a ranar bikin ka. Kar ka je kusa da shi domin kar ya dame ka. Barkono ya iya damun ciki, kuma ba abin da kana so a ranar kenan ba.

4. Fura da kindirmo: Wannan shi ne yogurt na gida wanda shi ne ya fi dadi sosai. Yana juya wa mafi yawan mutane ciki. Komai sabawarka da nono, ka yi hankali da shi a ranar bikinka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan bidiyo na nuna amfani cin wanna abincin lambu kokwamba

Asali: Legit.ng

Online view pixel