An damke marubucin Sahara Reporters Omoyele Sowore, za'a bankado shi Najeriya

An damke marubucin Sahara Reporters Omoyele Sowore, za'a bankado shi Najeriya

A daren jiya ne a birnin New York aka damke marubucin jaridar Sahara Reporters kuma ana shirin dawo da shi Najeriya

An damke marubucin Sahara Reporters Omoyele Sowore, za'a bankado shi Najeriya
Marubucin Sahara Reporters, Omoyele Sowore

Omoyele Sowore ya shiga rikici ne yayinda wani jami'in dan sanda yazo bashi karar da Dino Melaye ya shiga. Da ya fara mujadala da jami'in, sai yan sandan New York suka dauke shi kuma suka tsare shi.

KU KARANTA: Shin wanene ministan ilimin Najeriya?

Omoyele Sowore dai ba dan kasan Amurka bane kuma hukumar shiga da fice na shirye da fitar da mutane daga kasar kan karamin laifi.

A yanzu dai, lauyoyin Sahara Reporters na Kokarin zuwa inda aka tsare shi domin neman sasantawa da alfarma kada a dawo da shi.

Majiya na nuna cewa za'a dawo da shi gobe ta hanyar jirgin Arik zuwa Abuja, Najeriya. Kuma akwai labarin cewa hukumar DSS na kokarin kama shi idan ya sauka a jirgi.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel