Toh fa! Duba wannan wasika da Ibrahim Magu ya rubuta zuwa ga mai jeridar Sun
- Fred Itua, James Ojo da Lawrene Enyoghasu, "da gangan da kuma keta suka sanya ƙarya, hallakaswa, kalamai
- Marubutun ya yi rahoton ne da babu cikeken tushe , ya zargi cewa shi Magu ya mallaka kasaita 2
Mukaddashin shugaban Hukumar na Laifukan tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, yana neman wani gidan jarida (SUN) ta biya N5 biliyan ramuwa, domin " kalamai na bata suna" wanda jeridar ta yi game da shi a wani labari da aka buga a ranar 25 ga watan Maris, 2017 acikin ‘SUN na 'Asabar’.
Labarin ya je aka, "Magu karkashin sabon Bincike kan kasaita gidaje 2 a Abuja". Magu ya rubuta wa jeridar SUN, yana neman a biya shi biliyan N5 na diyya akan wannan.
KU KARANTA: Ba zamu bayyana kudin da aka kashe wajen jinyan Buhari ba - Gwamatin tarayya
A wata wasika mai kwanan rana Maris 30, 2017, wanda Magu ya aika wa wallafan ta hannu lauya sa, Wahab Shittu, ya lura cewa, marubuta labarin - Fred Itua, James Ojo da Lawrene Enyoghasu, "da gangan da kuma keta suka sanya ƙarya, hallakaswa, kalamai" gāme da shi.
Marubutun ya yi rahoton ne da babu cikeken tushe , ya zargi cewa shi Magu ya mallaka kasaita 2 waje daban-daban yankin Maitama, Abuja, wani hali wanda ba su tabbatar, wanda kuma ƙarya ne, kuma bãbu komai sai kwatancen tunaninsu.
Yadda rahoto da Legit.ng sun samu, ya kara tabbatar cewa "Da shi, da kuma matarsa basu mallaki dukiya ba a Maitama." Banda N5 biliyan na ramuwa,Magu ya bukaci wallafan su buga uzuri da kowa zai gani ko su karyata labarin nan da kwana 7.
KU KARANTA: Rikicin kabilanci: Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Yarbawa
Za su kuma rubuta tabbacin cikin kwanaki 7 da cewa za su daina bata ma Magu suna, kuma mutunci da kalamai su, ko kuma na ɓangare wasu.
Magu ya bukaci "nan da nan su karyata rubucensu daga wadannan kalamai ƙarya bata suna ", nan da kwana 7, kuma dole ne za a buga a kan gaban shafi na jaridar. Idan kuma suka gaza, sai sun fiskanci kotu. Har da diyyar kudi.
Magu caje wallafan su buga uzuri da kowa zai gani ko su karyata labarin nan da kwana 7.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wannan bidiyo na nuna wani da ba ya tsoro, shi ya fi karfi a Najeriya
Asali: Legit.ng