Gwarzon ɗan wasan Arsenal ka iya komawa Atletico Madrid

Gwarzon ɗan wasan Arsenal ka iya komawa Atletico Madrid

Rahotannin sun bayyana cewa kungiyar Atletico Madrid dake kasar Sifenna cigaba da nuna muradin siyan shahararren dan wasan Arsenal Alexis Sanchez a karshen kakar wasa.

Gwarzon ɗan wasan Arsenal ka iya komawa Atletico Madrid
Alexis Sanchez

A baya dai Sanchez ya buga ma kungiyar Barcelona wasa, kuma a yanzu kocin kungiyar Aletico Diego Simeone ya sa ido akan dan wasan tare da nuna muradinsa a fili musamman idan dan wasan ya amince da barin Arsenal.

KU KARANTA: Jami’an yansanda sun ceto tsohon minista daga hannun masu garkuwa da mutane

Sai dai a yanzu haka kungiyar Atletico na fuskantar talala daga siyan yan wasa wanda hukumar kwallo ta duniya, FIFA ta maka mata, amma duk da haka suna sa ran idan an daga musu talalar, zasu sayi sabon dan wasa a karshen kakar bana, kuma suna sa ran siyan Sanchez.

Sanchez mai shekaru 28 yana da suaran kwantaragi da kungiyar Arsenal har zuwa shekara ta 2018, kuma har yanzu yaki sake rattafa hannu kan sabon kwantaragi a kungiyar, wanda hakan ke nuni ga cewa Aresenal zata iya siyar da shi a karshen kakar wasan bana, idan ba haka kuwa zasu yi asarar rashin siar da shia a shekarar 2018.

Gwarzon ɗan wasan Arsenal ka iya komawa Atletico Madrid
Diego Simeone

A kwana kwanan nan Legit.ng ta ruwaito Sanchez yana fadin yafi so ya zauna a kungiyar Arsenal ya karasa kwantaraginsa, amma ya tabbatar da cewa yana bukatar yin wasa kungiyar dake samun nasarori a wasanninta.

Shima mao horar da kungiyar ATletico Diego Simeone ana sa ran kwantaraginsa zai kare a shekarar 2018, amma alamu sun nuna zai iya kara rattafa hannu, don haka ne yake son siyan Sanchez saboda ya taba wasa a gasar LaLiga, kuma ya iya cin wasanni.

Amma fa wani hanzari ba gudu ba, duk kungiyar dake muradin siyan Sanchez sai ta sauke pan miliyan 58 karanci, wanda a yanzu ba kowane kungiya bace zata jure siyansa kan wannan kudin. A yanzu haka akwai kungiyoyi da suka hada da PSG, Juventus, Bayern da Chelsea cikin wadanda ke neman siyan dan wasan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan baka kalli wasan Najeriya da Sanigal ba, kalla a nan:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel