An binne wata jaririya da ranta, amma tsilla-tsillarta ya cece ta (Hotuna da bidiyo)
Wani bidiyo mai ban tausayi ya yawaita a kafafen sadarwa na zamani inda aka hangi wata jaririya da ake ceto bayan an binne ta da ranta a cikin bola kasar India.
Rahotannin da Legit.ng ta samu ya bayyana cewar wata karamar yarinya ne ta lura da kafar jaririyar yana fitowa daga cikin kasa, nan san an ta kwala ihu, sai yan kauyen suka taru, inda suka hako inda suka ga kafar ke fitowa, abin mamaki sai suka yi arba da jaririya.
KU KARANTA: An kai ma ɗaliban Najeriya hari a ƙasar India, an raunata 5 (Hotuna)
Yan kauyen basu yi wata wata ba suka garzaya da jaririyar asibiti, inda a nan ne likitoci suka tabbatar da cea jaririyar bata wuce awanni 6 da haihuwa ba, kamar yadda kaakakin asibitin Fanindar Kumar ya bayyana.
Kumar ya shaida ma manema labaru cewar jaririyar na cikin koshin lafiya, kuma nauyinta ya kai kilo 2.5, sai dai ba’a yanke mata cibi ba
Ma’aikatan asibitin sun sanya ma jaririyar suna ‘Dharitri’, ma’ana ‘Kasa’ da yaren indiyanci, kuma sun bayyana cewar da zarar Dharitri ta kammala samun sauki, zasu mika tag a hukumomin kula da yara.
Sai dai wani bincike da yansanda suka gudanar ya nuna iyayen jaririyar sun yar da ita ne sakamakon basa son yarinya mace, namiji suke son haifa, ko kuma don bata hanyar aure aka same tab a.
Kasar India tayi kaurin suna wajen nuna bambamcin jinsin dan adam, sakamakon yawa da mata suka yi a kasar, inda bincike ya nuna ana samun mata 974 a duk haihuwa 1000. Wannan ne ya sa ake yawan zubar da ciki sa zarar an gano mace za’a haifa, tare da cin zarafin mata.
Wani rahoto ya bayyana an zubar da cikin jarirai mata guda miliyan 12 a shekaru 30 da suka gabata.
Ga bidiyon jaririyar nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng