Aliyu, ɗa ga Alhaji Buba Galadima ya rasu

Aliyu, ɗa ga Alhaji Buba Galadima ya rasu

Shahararren dan siyasan nan Alhaji Buba Galadima, kuma tsohon sakataren jam’iyyar CPC yayi babban rashi sakamakon rasuwar yaronsa mai suna Aliyu Buba Galadima sakamakon hadarin mota.

Aliyu, ɗa ga Alhaji Buba Galadima ya rasu
Marigayi Aliyu Buba Galadima

Marigayi Aliyu ya rasu ne a ranar Lahadi sakamakon hadarin mota daya auku tsakanin motoci 6 a kan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja, yayin dayake kan hanyarsa ta komawa Abuja.

KU KARANTA: "Musabbabin rikicina da Dangote" – Gwamna

Yayar Ali, Zainab Buba Galadima ta bayyana ma jaridar Daily Trust cewa marigayin yayi tafiya zuwa Kaduna don ganin matarsa Hadiza, a lokacin dayake kan hanyarsa ta dawowa ne ya gamu da hatsarin motar.

“Ba Aliyu bane ke tuka motar, su hudu ne a cikin motar. Tayar wata mota ce ta fara fashewa, inda motar ta kufce ta afka ma saura motoci guda hudu ciki har da motar da Aliyu ke ciki, Aliyu kadai ya mutu nan take, a yanzu abokanansa suna samun kulawa a asibiti.

“Ko a shekarar 2004 ya taba yin hadari akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda jama’a suka dauka ma ya mutu, har na fara daura masa ganye a gefen hanya, kafin daga bisani Allah ya dawo masa da ransa.

“Kamar yasan zai rasu, don ko a ranar Lahadin sai daya shaida ma matarsa idan ya mutu ita yake so tayi masa wankan gawa,” inji Zainab.

Jama’a da dama sun halarci sallar jana’izar Aliyu Buba Galadima daya gudana a masallacin Annur, wasu kuma sun je gidan Alhaji Buba Galadima dake titin Bangui don yi musu ta’aziyya.

Legit.ng ta ruwaito wasu daga cikin wadanda suka kai ziyarar ta’aziyyar sun hada da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Alhaji Yayale Ahmed, tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Abba Kyari, Ministan wasanni Solomon Dalung, sanata Rabiu Kwankwaso, Aliyu Shinkafi, Hajiya Khairat Gwadabe da kuma ministan ayyuka Baba Shehuri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon jirgin sama daga Kaduna zuwa Abuja, musamman ga wadanda basa son bin titin Kaduna zuwa Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel