Wasu jajirtaccin matasa sun kama wani tsoho da kam mutum

Wasu jajirtaccin matasa sun kama wani tsoho da kam mutum

- Rahotanni daga jihar Legas na bayyana cewa, wasu matasa sun kama wani mutum mai kimanin shekaru 61 mai suna Taoofiq Hassan, da sassan jikin mutum sabon yanka, bayan sun lura buhun da yake dauke da shi yana digar da jini

- Sai dai bayan takura shi ya fitar da abin da ke cikin buhun an ga sassan jikin wata matashiyar budurwa, da suka da kai, zuciya da hannaye

Wasu jajirtaccin matasa sun kama wani tsoho da kam mutum
Jami'in yan sanda yana yiwa yan jarida bayani

Matasan sun yi wa mutumin dukan kawo wuka, inda suka daure shi suna jan sa a kasa, sai da jami'an tsaro daga ofishin 'yan sanda na Area K suka kai dauki wajen, suka kwace shi da rai.

Binciken 'yan sanda ya gano cewa, matar wacce ba a ambaci sunan ta ba ta je wajen wani mai magani ne da ake kira Baba Ronke, domin neman taimako game da wasu matsaloli da ta ce tana fuskanta, shi kuma mai maganin ya hada ta da wani malami da aka ambata da Alfa wanda yake Sango-Otta, inda aka ce yana tsafi da sassan jikin mutane.

KU KARANTA: Da ba don Buhari ba da yanzu Mun zama tarihi - Gwamna

Shi dai Taoofiq da aka kama ya ce, mutanen biyu ne suka yaudari matar suka kai ta Badagry inda suka yi mata karyar za su hada ta da wani babban masanin magunguna dake bakin ruwa. Alhalin kuwa sun biya shi idan ta zo ya kashe ta, ya kai musu sassan jikin ta.

Ya ce, a hanyar sa ta kai musu abin da suka nema ne wasu matasa suka tare shi a hanya, yayin da asirin sa ya tonu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli wasu mata masoya Buhari na yin gangami a Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng