Kaji mummunar badakalar da ta bullo a hukumar ma'aikatan gidan yari?

Kaji mummunar badakalar da ta bullo a hukumar ma'aikatan gidan yari?

Wani bincike da wata kafar yada labarai ta gudanar kuma kamfanin Legit.ng ya samu ya bankado wata babbar badakala ta daukar aiki a sirrance da ke guda a hukumar ma'aikatan gidan yari ta kasa.

Kaji mummunar badakalar da ta bullo a hukumar ma'aikatan gidan yari?
Kaji mummunar badakalar da ta bullo a hukumar ma'aikatan gidan yari?

Binciken dai ya nuna cewa yanzu haka ana daukar aiki a hukumar a sirrance inda kuma wasu masu bukata kan biya zunzurutun kudin da suka kai N650,000 na rashawa kafin a dauke su aikin.

KU KARANTA: Abu 3 da baku sani ba game da Buhari da Burutai

Binciken har ila yau ya ce kawo yanzu an dauki mutane a hukumar sama da 3,800 wanda kuma yanzu haka har an tura su inda za suyi aiki bayan sun gama amsar horo na musamman.

Majiyar tamu ta bankado cewa ana tambayar masu takardar shedar karatu ta digiri su bada N650,000 su kuma masu difloma suna bada N550,000 sannan kuma wadanda ke da shedear sakandare sukan bada N400,000 kafin a dauke su din.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng