Karanata munanan matsalolin shan sigari guda 6, na farko zai tada maka hankali
- Wani rahoto da Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta wallafa, ya ce akwai kimanin 'yan Najeriya miliyan 13 da ke shan taba sigari
- Binciken da hukumar ta yi ya nuna cewa mafi yawancin mashayan maza ne
- Bisa kiyasin rahoton, kamfanonin taba sigari a Najeriyar na samun cinikin naira biliyan 90 a duk shekara
An dai ce Najeriya da Misra da Afirka ta Kudu ne ke kan gaba wajen yawan mashaya taba sigari, a duniya.
Farfesa Musa Baba Shami wani kwararren likita ne a fannin cututtukan huhun dan adam, a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kanon Najeriya.
KU KARANTA: An dakatar da basarake saboda laifin fyade
Ya kuma danganta karuwar kasuwar taba sigari a kasashen Afirka da "dokoki masu zafi a kasashen turai da ke sanya kamfanonin tabar su shiga Afirka inda akwai karancin irin wadannan dokoki."
Farfesa Shami ya kuma ce akwai illoli da shan taba sigarin yake yi wa jikin dan adam da suka hada da:
1. Gadar wa mai shan taba cutar kansa
2. Makanta
3. Cutar suga
4. Bugawar zuciya
5. Matsalar numfashi
6. Yawan tari
Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta ce an sami raguwar zukar taba sigari da kashi bakwai cikin dari a yankunan Turai da kudancin Amurka sakamakon daukar wasu matakai.
KU KARANTA: Bangarorin PDP sun hallara kotu don yin fadan karshe
Matakan kuma sun hada da tsawwala haraji kan taba da tilasta rubuta gargadin hadarin shan tabar da kuma hana tallata ta a kafofin watsa labarai.
Sai dai kuma WHO ta ce an sami karuwar shan tabar da kashi 12 cikin 100 a nahiyoyin Afirka da Asiya, inda ba a bin wadancan matakai.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng