Soyayya: da gaske ne wannan gwamnan ya zama ‘mijin tace’?

Soyayya: da gaske ne wannan gwamnan ya zama ‘mijin tace’?

Soyayya ya debi gwamnan jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun, inda yayi ma matarsa wani abun ban sha’awa daya kamata mazaje su yi koyi da shi a ranar Laraba 22 ga watan Maris.

Soyayya: da gaske ne wannan gwamnan ya zama ‘mijin tace’?
Soyayya: da gaske ne wannan gwamnan ya zama ‘mijin tace’?

Gwamnan yayi wannan bajinta ne bayan ya halarci taron kungiyar mata na ‘Women Arise’ inda aka gangamin nuna bacin rai da yadda wasu mazaje ke cin zarafin matayensu a garin Abekuta na jihar Ogun.

Bayan gwamnan ya kammala jawabin nasa ne, sai jama’an da suka halarci taron suka fara yi masa barka tare da tafi suna jinjina masa, daga nan kawai sai ya shiga motarsa tare matarsa, sa’annan ya tuka ta suka wuce gida, sauran yan tawagar nasa suna binsa a baya.

KU KARANTA: An gano gidan alfarma na £2,000,000 a ƙasar Ingila mallakin tsohon babban hafsan sojan sama

Soyayya: da gaske ne wannan gwamnan ya zama ‘mijin tace’?
Soyayya: da gaske ne wannan gwamnan ya zama ‘mijin tace’?

Ana yawan samun matsalolin cin zarafin mata a kasar nan, hakan ne yasa gwamnan ya nuna ma mazaje yadda ya kamata su dinga kulawa da matayensu, dalilin dayasa kenan aka shirya wannan gangami.

Gwamnan yaci alwashin zasu hukunta duk namijin da aka kama da laifin cin zarafin matarsa a jihar Ogun, don ma kada su ji da wai, sai ya tuka matarsa har gida.

Ga bidiyon gwamnan nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng