An kashe akalla mutum 32 a Zaki Biam ta Benue
- A kalla mutum 32 ne suka mutu a garin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum na jihar Benue, da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya
- Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari wata kasuwar doya a garin Zaki Biam da ke jihar
Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Moses Yamu ya ce mutum 17 ne suka mutu yayinda wasu 11 suka jikkata.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin, ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa ga 'yan uwan wadanda harin ya shafa.
KU KARANTA: Darajar Naira ta kara yin sama
Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ya ce: "Shugaba Buhari ya umarci jami'an tsaro su fara binciken gaggawa da nufin hukunta wadanda suka aikata laifin."
Moses Yamu ya shaida wa majiyar mu cewa: "Da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin ne wasu mutane a cikin mota da kuma wasu a kan babura suka shiga garin kuma suka bude wa wasu 'yan kasuwa wuta."
Ya kara da cewa tuni an kara tsaurara matakan tsaro a yankin kuma tuni aka kama mutum uku wadanda ake zargin suna da hannu a harin.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng