An damke Khaleel Tanko Al Makura akan laifin kisan kai
An damke Mr. Khaleel Umar Al-Makura, haifaffen cikin gwamnan jihar Nasarawa, Umar Al-Makura akan laifin kisan wani dalibin makarantan gwamnati mai suna Ovye Amos, a Lafia.
Wani abun takaici ya faru ne a ranan Litinin a hadarin mota. Sai daliban makarantan suka fara zanga-zanga a ranan Talata domin neman a hukunta wanda kashe dalibin makarantan sakandaren.
Amma jami’ an tsaro sun yi magana da daliban domin kashe wutan abinda ya faru.
KU KARANTA: Majalisar dattawa zata fara binciken Melaye da Saraki
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Kwamishanan ilimin jihar, Aliyu Tijjani, ya fadawa daliban cewa gwamnati zata dau matakin da yakamata wajen tabbatar da cewa an hukunta yaron gwamann da ya aikata wannan abu.
“An damke shi, kuma ina mai nuna bacin raina akan abinda ya faru jiya. Abin takaici ne, da takaici sosai.”
Shugaban daliban makarantan, Goodluck Agwu, yayi bayanin cewa motar Mr. Khaleel Umar Al-Makura, ta bige yaron ne yayinda yaje sayan batirin fitilarshi.
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng