Hassan Lemu: Babban sakataren Sardauna ya rasu yana da shekaru 95
Allah yayi wa Alhaji Hassan Lemu tsohon babban sakataren firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardauna rasuwa a garin Minna da misalin karfe 8:45 na dare yana da shekaru 95.
Daya daga cikin yayansa mai suna Salihu Hassan Lemu ne ya sanar da rasuwar mahaifin nasu, inda yace yayi fama da ciwo, hakan yasa suka mika shi asibiti don samun kulawa, a can ya cika.
KU KARANTA: Kungiyar Izala zata gina cibiyar koyar da sana’o’i
A satin daya gabata ne jaridar Daily Trust ta dauko rahoton cewar gwamnatin tarayya ta biya shi bashin fansho dayake bi na tsawon shekaru 6, hakan kuma ya faru ne sakamakon wani rahoto da jaridar ta buga inda ta bayyana cewar an dakatar da biyansa fansho nasa.
A shekarar 1949 ne Hassan Lemu ya shiga aikin gwamnati, inda yayi ayyuka da dama a birnin Landan da Najeriya, a shekarar 1956 ne aka tura shi ofishin Sardauna dake Kaduna a matsayin babban sakataren sa. Daga nan sai aka nada shi mukamin mataimakin jami’in lardi (ADO) watan Disamnar 1956, inda aka tura shi jihar Borno, bayan nan ya sake komawa ofishin kwamishinan Arewa a birnin Landan a matsayin sakatare a watan Mayu na shekarar 1957.
Daya dawo Najeriya a watan Yuli na 1960, sai aka sake mayar da shi ofishin Sardauna, daga bisani kuma ya zama sakataren dindindin a ma’aikatar shari’a a shekarar 1961. An sake tura shi Borno a matsayin sakataren lardi, bayan nan ne ya sake dawowa ofishin Sardauna a shekarar 1964 har zuwa 1966.
A shekarar 1974 ne Hasssan Lemu yayi ritaya a matsayin sakataren dindindin a ma’aikatar kudi, mamacin ya rasu ya bar yara 24 da jikoki da dama, kuma anyi jana’izarsa a babban masallacin garin Minna, wanda babban limamin masallacin Alh Isah Fari ya ja.
Cikin wadanda suka samu halartan jana’izar tasa akwai mataimakin gwamnan jihar Neja Alhaji Ahmed Muhammed Ketso, Sarkin Minna Alhaji Umar Bahago, sarkin Agaie Alhaji Nuhu Yusuf.
Allah ya jikansa da gafara
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng