Bayan likita ya afka tekun Legas, an ceto wata mata da ta fada yau (Hoto)

Bayan likita ya afka tekun Legas, an ceto wata mata da ta fada yau (Hoto)

Wata mata tayi kokarin kashe kanta a jihar Legas ta hanyar fadawa cikin tekun Legas daga kan gadan Maza-Maza na Mile 2

Bayan likita ya afka tekun Legas, an ceto wata mata da ta fada yau( Hoto)
Bayan likita ya afka tekun Legas, an ceto wata mata da ta fada yau( Hoto)

Game da cewan idanuwan shaida, matar na sanye da kananan kaya tana tafiya kan gadan kawai sai ta fada cikin tekun da gangan.

Wasu mutanen da ke kusa da wurin suka fada tekun domin ceto ta. Bayan sun fitar da ita, sai aka fara danne cikinta domin fitar da ruwan da ta sha.

KU KARANTA: An damke wacce ta jefa jariri masai

Wani idon shaida mai suna Emeka yace: “Abun ya faru da wuri ne ta yanda bamu iya hanata ba. amma lokacin da ta fada, sai mukayi kira aka ceto ta."

Wani daga cikin wadanda suka ceto ta Adewale yace: “ Muna karkashin gadan, kawai sai muka ga mace ta fada cikin ruwa. Da farko munyi tunanin wani ne ya tura ta ko ta fadi da kuskure.”

Wannan abu na faruwa ne bayan wani likita ya kashe kansa ta hanyar fadawa cikin teku a jiya.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng