Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai

Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai

Ga masu son shiga kwalejin horar da hafsan yansanda dake wudil, toh lokaci yayi da zasu nemi hurumin shiga wannan makaranta, ana bukatar masu nema dasu garzaya zuwa wannan shafin yanar gizo www.polac.edu.ng don samun lambar Remita, wanda zasu yi amfani dashi wajen biyan kudi N3000 a kowanne banki dake Najeriya.

Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai
Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai

Ana bukatar masu nema dasu tabbata sun samu sakamako mai kyau a jarrabawar JAMB, sai dai ba lallai sai ka zabi kwalejin a cikin jerin muradun ka na JAMB ba, ko baka zabi kwalejin ba zaka iya nema, ana kara jaddada ma masu nema daus tabbatar sun samu sakamako mai kyau, domin da wannan ne kawai za’a basu daman zana jarabawar neman shiga kwalejin.

Idan mai nema ya shiga shafin yanar gizon da aka bayyana a sama, sai ya aika da sakonnin daya cike, bayan nan za’a aika ma duk wanda ya cancanta takardar cikewa na neman izinin iyaye.

KU KARANTA: An yi ragas, yayin da Uba da ɗa suka afka cikin rijiya, dukkansu suka mutu a jihar Sakkwato

Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai
Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai

Ka’idar neman shiga wannan kwalejin sune: mutum ya kasance dan Najeriya, shekarun ka ya kasance tsakanin 17 zuwa 22, tsawonka ya kasance tsakanin 1,67 zuwa 1.62, sa’annan ba’a yarda nakasashshe ya nema ba.

Bugu da kari dole ne mai nema ya samu sakamako mai kyau daga jarabawar WAEC ko NECO ko NABTEB, ciki har da Ingilishi da lissafi, sa’annan dole ne mai nema ya samu sakamako mai kyau a jarabawar da za’a gudanar na gwajin lafiyar jiki, jarabawar rubutu da na hankali.

Sai dai akwai daman zabi a irin jarabawar da mai nema ke son zanawa na shiga kwalejin, imma dai a jarabawar takarda ko na kwamfuta, jarabawar kuma ta hade dukkanin fannonin karatu kamar su Turanci, lissafi, sai sauran fannonin da suka danganci sha’awar dalibi.

Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai
Kwalejin horar da hafsan ýansanda dake Wudil zata fara ɗaukan ɗalibai

Za’a yi jarabawar ne a ranar Asabar 8 ga watan Yuli 2017, kuma za’a yi jarabawar a cibiyoyi guda 12 a duk fadin kasar nan, jerin cibiyoyin zana jarabawar na nan a shafin yanar gizo na kwalejin yansandan, ana bukatar duk wanda aka gayyata zana jarabawar daya hallara akan lokaci kuma yazo tare da hotunan fasfo guda 2, sai a rubuta suna da shekaran haihuwa da garin haihuwa, cibiyar jarabawa da sa hannu duk a bayan fasfon.

Bayan jarabawar za’a gayyaci duk wanda ya samu nasara a jarabawar don sake tantance su, daga nan sai a buga sunayen wadanda aka zaba bayan tantancewa a jaridu da kuma shafin yanar gizon kwalejin. Duk wanda aka zaba, zai smau damar samun digiri bayan shekaru 5 daga kwalejin yansanda dake Wudil, jihar Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng