Yadda wata budurwar karuwa ta koma tsohuwa da rana tsaka (Hotuna)

Yadda wata budurwar karuwa ta koma tsohuwa da rana tsaka (Hotuna)

- Wani mutum ne ya tsaya ya dauki wata budurwa kyakyawa irin wadanda suke tsayawa a kan hanya maza su zo su dauke su, ya kai ta gidansa

- Suna tare a gidansa har na tsawon kwanaki uku, a ranar cikon kwanakin ukun ne ya shiga makewayi domin ya yi wanka, yana fitowa sai ya samu wannan tsohuwa tana kwance a kan gado sai gabansa ya fadi

Yadda wata budurwar karuwa ta koma tsohuwa da rana tsaka (Hotuna)
Yadda wata budurwar karuwa ta koma tsohuwa da rana tsaka (Hotuna)

Ya tambaye ta wacece ita, ita kuwa ta ce ita ce dai wadda ya shiga wanka ya bari, wanda suka yi kwana uku tare nan ne ya musanta mata cewa shi sam bai santa ba.

Nan ta ce masa zai mutu sai ya kamata da duka tare da kira mata jama'a inda suka tasa mata keyarta zuwa ofishin 'yan sanda a Younde da ke kasar Cameroon.

Tun kafin su tafi ofishin 'yan sanda, ta ke ce mashi, "abunda nake so na tabbatar maka kar ma ka gaji da dukana za ka mutu ne."

A wajen 'yan sanda din ma maganarta daya take ta nanatawa, "zai mutu" tana cikin nanata hakan ne ya fadi ya mutu, kowa ya watse a guje.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng