Dandalin Kannywood: Rahma Sadau ta jinjinawa Ali Nuhu da wannan (Karanta)

Dandalin Kannywood: Rahma Sadau ta jinjinawa Ali Nuhu da wannan (Karanta)

-Yau ne fitaccen jarumin finafinan Hausa Ali Nuhu ke murnar zagayowar haihuwarsa a inda masoya suka yi ta aike masa da sakon taya murna wannan rana

-A nata sakon Rahma Sadau ta ce jarumin ya cancanci yabo da kuma jinjina saboda irin rawar da ya ke takawa a finafinan Hausa

Dandalin Kannywood: Rahma Sadau ta jinjinawa Ali Nuhu da wannan (Karanta)
Rahma Sadau ta jinjinawa Ali Nuhu tare da kiransa 'Maharaja', Sarki

A yau 15 ga watan Maris ne jarumin finafinan Hausa Ali Nuhu ke murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Tuni dai jarumin ya soma samun sakon taya shi murna zagayowar wannan rana, rututu daga 'yan uwa da abokan aiki, da kuma sauran masoya.

A sakon Rahama Sadau na taya murnar ga jarumim, wanda ta kuma lika a shafinta na dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook, ta na mai cewa, "ina mai taya 'Maharaja' " watau sarki da yaren indiya, "Ali Nuhu murnar zagayowar wannan rana".

Sannan ta kuma ce, "ina kuma fatan Allah Ya maimaita mana wannan rana, ta zo cike da alheri, da kuma nasarori masu yawa".

Sauran abokan aiki a masana'antar shirya finafinai na Kannywood suma sun aika da sakwanninsu.

Yakubu Mohammed mawaki kuma jarumi a finafinan Hausa da na kudancin kasar nan, a nasa sakon a shafin Ali Nuhu ta dandalin sada zumunta na Instagram, ya taya jarumin murna da kuma yi masa fatan alheri.

Sai dai Jarumi Ali Nuhu bai bayyana ko zai yi shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar tasa ba kamar yadda sauran 'yan wasan Hausa suke yi.

Da akwai dangantakar aiki mai karfi tsakanin Rahma Sadau da kuma Ali Nuhu wanda wasu ke cewa shi ne ya fara sa ta a fim a 'yan shekarun baya.

A baya dai jarumi Ali Nuhi, wanda masoyansa ke yiwa lakabi da 'Sarki' a shirin finafinan Hausa, ya yi kokarin sa baki a hukuncin korar da kungiyar MOPPAN ta yiwa Rahma Sadau daga fitowa a finafinan Hausa, wanda kuma shi ne sadiyyarta barin kasar nan a shekarar 2016.

Mu ma a Legit.ng muna taya Ali Nuhu murnar zagayowar wannan rana.

Ga bikin murnar dawowar Buhari a garin Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel