An kafa sabuwar rundunar sojan ruwan Najeriya a Arewa
A ci gaba da yi wa ‘yan kungiyar Boko Haram kofar rago don hana su damar shagar da makamai Najeriya, hedikwatar sojojin ruwa ta kafa sabuwar runduna a tafkin Chadi don tabbbatar da tsaro.
An gano cewa ‘yan Boko Haram na shigar da makamai cikin Najeriya daga ruwan tafkin chadi, hakan yasa gwamnatin tarayya ta umarci sojojin ruwa da su bude runduna a gurin, a cewar daraktan labarai a hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Kaftin Sulaiman Dahun.
KU KARANTA: An gano gunkin Firauna a kasar Misra
Baya ga tafkin Chadi, rundunar sojan ruwan ta kuma kakkafa ‘karin wasu rundunonin a sauran sassan Najeriya. Haka kuma rundunar ta yi tunanin bude sabbin rundunoni a duk inda ake da babban kogi a fadin kasar.
Masanin tsaro Saleh Jingir mai ritaya, ya ce kafa runduna da sojojin ruwa su kayi a yankin tafkin Chadi wani abu ne mai matukar muhimmanci, ganin yadda ake amfani da ruwan wajen shigar da makamai.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng