Ko me Ganduje ke ginawa a kan babban titin birnin Kano?

Ko me Ganduje ke ginawa a kan babban titin birnin Kano?

-Gwamnan Kano ya ja hankalin Kanawa da wasu sabbin gine-gine masu kama da hasumiya a kan babban titi zuwa gidan gwamnati daga kofar Nassarawa

-Gwamnan ya kaddamar da shirin karkara fes lunguna kal-kal a yunkurinsa na kawata jihar Kano birni da kauye.

Ko me Ganduje ake ginawa a kan babban titin birnin Kano?
Ko me Ganduje ake ginawa a kan babban titin birnin Kano?

Mutanen Kano na cike da zakuwa na sanin ma'anar wasu sabbin gine-gine da ake yi masu kama da hasumiya a kan babban titin 'State road' da ke tsakiyar babban birnin jihar.

Mutane na mamakin me kuma titin da ya fi kowanne kyau a jihar ke bukata, har ake wadannan gine-gine ganin yadda a baya ya sha kwaliya da kyale-kyale daga gwamntocin da suka shude.

Yayin da wasu ke cewa ana yi ne don samar da wuta mai amfani da hasken rana a kan titin, wanda tuni ke da manya-manya fitulu masu aiki da injin janareto.

Wasu kuma na cewa ana yi ne don kara kawata titin da ya ke daya tilo daga gidan gwamnati zuwa fadar mai martaba Sarki, kamar yadda wakilin Legit.ng ya ganewa idonsa.

Sai dai yayin da wani mai sharhi a dandalin sada zumnuta na Facebook, Umar Lawan ke cewa,"ginin dogo ne maras fadi da ake yi da bulo mara kwari alama ce ta annoba."

Shi kuma wani mai sharhin, Ibrahim Bargoni cewa ya ke yi, "rumfa za a yi wa titin".

Ko me Ganduje ake ginawa a kan babban titin birnin Kano?
Daya daga cikin turakun da ke jan hankalin mutane a Kano

Jaridar Daily Nigerian ta raiwaito cewa, ba wai masu tafiya a kafa kadai abin ya daure wa kai ba, har da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar, su ma ba su san abin da gwamnan ke shirin yi ba a kan babban titin.

A cewar wani makusancin gwamnan."Mun sha tambayarsa kan wannan gini amma sai ya ce da mu jira har sai an gama aikin. Masu aikin ne kadai da wasu 'yan tsirarun jami'an gwamnati su ka san abin da gwamnan ke shirin yi,"

Ko me Ganduje ake ginawa a kan babban titin birnin Kano?
Kwaliyar da ake tunanin Ganduje ke shirin yiwa titin gidan gwamna irin na jihar Imo

Ginin mai kama da hasumiya ana yin sa kamar durkokin ne ta kowane bangare a gefen titin da kuma tsakiya.

Zanga-zangar goyon bayan Buhari a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng