Yan mata 8,000 za su koma makaranta a jihar Katsina da taimakon UNICEF

Yan mata 8,000 za su koma makaranta a jihar Katsina da taimakon UNICEF

- An dibi yaran da za su ci amfani kudin ne daga ciki yaran talakawa da basu da karfin tura yara makaranta

- Wannan abin da UNICEF suka yi ya nuna sun san muhimincin yara mata su yi makaranta

- Ko wace yarinya zata kashe N20,000 acikin kudin domin siyan takardan makaranta, kaya makaranta, abubuwar na rubutu da sauran abin da suke bukata

Yan mata 8,000 za su koma makaranta a jihar Katsina da taimakon UNICEF
Yan mata 8,000 za su koma makaranta a jihar Katsina da taimakon UNICEF

Hukumar UNICEF sun taimaka wa yan mata 8,000 a jihar Katsina da adin kai da hukuma karatu na jihar, wato ‘State Universal Basic Education Board’ (SUBEB).

UNICEF sun yi wannan taimako na tura mata 8,000 makaranta garin bada milyan N160 ma SUBEB na Katsina.

Ciyaman na SUBEB a Katsina, Alhaji Lawal Buhari ya nuna farin ciki, yana magana a Daura ranar Talata cewar, kudin zai yi nisa wajen taimaka wa karatun yan matan.

Inji shi wai ko wace yarinya zata kashe N20,000 acikin kudin domin siyan takardan makaranta, kaya makaranta, abubuwar na rubutu da sauran abin da suke bukata.

KU KARANTA: Zahra Buhari ta yi magana game da soyayyar da mahaifinta key i ma Najeriya (HOTUNA)

Ya kara bayyana cewar, an dibi yaran da za su ci amfani kudin ne daga ciki yaran talakawa da basu da karfin tura yara makaranta. Wai an dibi yaran ne daga makarantu karamin hukumar 34 a jihar.

Inji shi wai wannan taimakon UNICEF sun nuna suna yi ne na gaske wajen taimakon yara. “Mun kafa kwamiti da y raba kudin ma masu bukatan domin adalci. Wannan abin da UNICEF suka yi ya nuna sun san muhimincin yara mata su yi makaranta.”

Ya ba yaran shawara akan su san abin da su ke su kuma sa kai a karatu kar su yi wasa da rayuwar su na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng