Kisan Hausawa a Ile-Ife: Sanata Kwankwaso ya je bin ba'asi
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Ibadan inda ya shiga mota zuwa Oshogbo babban birnin jihar Osun domin ganawa da gwamnan Jihar Osun Alhaji Rauf Aregbesola dangane da kisan gillar da aka yi wa Hausawa a garin Ile Ife.
Bayan sun gama tattaunawa da gwamnan jihar Osun, yau da safe Sanata Kwankwaso zai nufi garin Ile Ife domin tattaunawa da Sarakunan gargajiya na masarautar Ife da nufin jin musabbabin wannan kisan gillar da aka yi wa Hausawa a garin na Ile Ife domin a zakulosu su fuskanci hukuncin abinda suka aikata.
A wani labarin kuma, Alamu na nuna cewa tsohon Gwamnan jihar Kano dake arewacin Najeriya Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya kammala shirin sa na komawa jam'iyyar PDP nan ba da dadewa ba.
Wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar ta Kano watau Alhaji Musa Iliyasu ne ya bayyana hakan a hirar su da gidan jaridar Daily trust a Kano.
A cewar sa: "Naji daga majiya mai tushen gaske cewa tsohon gwamnan da yanzu basu ga maciji da aminin sa kuma Gwamnan Kano na yanzu Umar Ganduje ya shirya tsaf domin ficewa daga jam'iyyar APC."
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng